NIJERIYA
3 minti karatu
Nuhu Ribadu ya mayar wa El-Rufai martani kan zargin cewa gwamnati na biyan 'yan ta'adda kuɗaɗe
Mai magana da yawun Ofishin Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro Malam Zakari Mijinyawa ya ce kalaman na tsohon gwamnan ba gaskiya ba ne.
Nuhu Ribadu ya mayar wa El-Rufai martani kan zargin cewa gwamnati na biyan 'yan ta'adda kuɗaɗe
A baya Nuhu Ribadu da Nasir El-Rufai abokan juna ne sosai. / Others
8 awanni baya

Ofishin Babban Mai Bai wa Shugaban Nijeriya Shawara kan Tsaro Malam Nuhu Ribadu ya mayar wa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai martani dangane da wata hira da El-Rufai ya yi da gidan talabijin na Channels TV ranar Lahadi.

Tsohon gwamnan, wanda ya fice daga jam’iyya mai mulki ta APC kuma ya koma hadakar ’yan adawa ta ADC, ya yi zargin cewa gwamnatin Jihar Kaduna tana biyan ’yan ta’adda makudan kuɗaɗe kuma tana neman gafararsu.

Ya ce lokacin da ’yan bindiga suka kai hari na farko a wata makaranta a Jihar Kaduna, sai da aka biya su naira biliyan daya kafin su sako ɗaliban da aka yi garkuwa da su.

Sannan ya yi ikirarin cewa idan gwamnan jihar ko duk wani da yake da shakku kan abin da ya fada, ya kalubalance shi, to zai fito da hujjojin da yake da su kan hakan.

El-Rufai, wanda ya mulki Jihar Kaduna tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023, ya zargi gwamnati da ƙarfafa wa ’yan bindiga gwiwa kuma ya ce babu inda aka taba yin haka kuma aka samu nasara a duniya.

Sai dai mai magana da yawun Ofishin Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro Malam Zakari Mijinyawa ya ce kalaman na tsohon gwamnan ba gaskiya ba ne.

Ya ce ba a taba samun wani lokaci da Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara, ko gwamnati a kowane mataki da ta taba biyan kudin fansa ga miyagu, masu aikata manyan laifuka ba, kamar yadda ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Malam Zakari Mijinyawa ya ce saɓanin yadda El-Rufai ke magana, ya ce Ofishin Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro yana yawan gargaɗin jama’a kan ka da su riƙa biyan kudin fansa ga ’yan bindiga.

Ya ce kalaman El-Rufai zarge-zarge ne da babu gaskiya a cikinsu kuma sun ci karo da sahihan bayanai da ke kasa, a cewarsa.

Malam Zakari ya ce tun daga farko gwamnati mai ci tana amfani da hanyoyi biyu ne wajen magance matsalar tsaro, wato amfani da ƙarfin tuwo da tattaunawa da al’ummomi ta yadda za a warware matsalar.

Ya ce sakamakon haka ne ya sa aka fara samun zaman lafiya a Igabi da Birnin Gwari da Giwa da wasu bangarori na Jihar Kaduna wadanda a baya suke fama da matsalar tsaro.

Sannan ya ce a daya bangaren sojojin kasar da sauran jami’an tsaro sun yi nasarar kama ko kawar da wasu manyan ’yan bindiga.

Mai magana da yawun Ofishin Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro ya bayar da misalin yadda a Jihar Kaduna  aka yi nasarar kawar da wasu jagororin ’yan bindiga kamar Boderi da Baleri da Sani Yellow Janburos da sauransu.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us