SIYASA
2 minti karatu
Trump ya ce yarjejeniyar Ukraine za ta iya taimaka masa 'shiga aljanna'
Shugaban Amurka ya ce yana fatan samun sa'ar shiga aljanna sakamakon ƙoƙarin da yake yi na samar da zaman lafiya tsakanin Ukraine da Rasha.
Trump ya ce yarjejeniyar Ukraine za ta iya taimaka masa 'shiga aljanna'
Trump ya ce yarjejeniyar Ukraine za ta iya taimaka masa 'zuwa aljanna' / AP
17 awanni baya

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Ukraine da Rasha za ta iya taimaka masa wajen shiga aljanna, yana mai yin barkwanci cewa damar samun makoma mai kyau a halin yanzu ba ta da yawa.

"Ina so na yi koƙari domin na shiga aljanna idan hakan zai yiwu" kamar yadda Trump ya shaida wa shirin safe na Fox News "Fox & Friends."

"Na amince cewa ba na yin abu mai kyau - ina ji a jikina cewa na kusa zuwa kabarina! Amma idan na samu zuwa aljanna, wannan zai zama ɗaya daga cikin dalilai.”

A baya dai shugaban, mai shekaru 79, ya sha alwashin kawo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine da kuma fatansa na lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya.

Kalamansa na baya bayan nan sun nuna sha’awarsa ta tafiya lahira fiye da zaman duniya.

Trump shi ne shugaban Amurka na farko da aka yanke masa hukunci laifi, wanda ya samo asali daga yunƙurin ba da cin hanci ga wata babbar ‘yar wasan kwaikwayo.

Sau biyu ana tsige shi, kana ya sha shiga badaƙala a rayuwarsa.

'Ceto daga Allah '

Duk da haka, Trump ya rungumi salon addini mai ƙarfi tun bayan da ya tsallake rijiya da baya a wani yunƙuri na halaka shi a bara.

A bikin rantsar da shi a watan Janairu, ya bayyana cewa "Allah ne ya cece ni don na sake mayar da Amurka babbar ƙasa."

A yanzu haka Trump na samun cikakken goyon baya daga masu ra’ayin addini na Amurka.

Ya naɗa Paula White a matsayin mai ba shi shawara kan lamuran addini, kana ya jagoranci tarurrukan addu'o'i inda mahalarta suka dafa kan shugaban a tarurrukan Fadar White House.

Sakatariyar yaɗa labarai, Karoline Leavitt, ta faɗa wa manema labarai a ranar Talata cewa ta yi amanna cewa da gaske Trump yake game da kalamansa na shiga aljanna.

"Ina jin shugaban yana son ya shiga aljanna, kamar yadda nake fata dukkanmu a cikin wannan ɗakin za mu shiga,” in ji ta.

Leavitt, mai shekaru 27, ta yi fice wajen jagorantar addu'o'i kafin taron manema labarai.

Trump ya ci gaba da jaddada cewa, kawo ƙarshen yakin Ukraine wata babbar manufa ce ta shugabancinsa, yana mai bayyana hakan ba kawai a matsayin aikin diflomasiyya ko na siyasa ba, amma a matsayin hanya ta samun tsira.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us