Zaluncin mulkin mallakar Faransa a Kamaru: Dalilin da ya sa ikirarin Macron zama ƙarya da gaskiya
AFIRKA
6 minti karatu
Zaluncin mulkin mallakar Faransa a Kamaru: Dalilin da ya sa ikirarin Macron zama ƙarya da gaskiyaAmincewar da Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi na zubar da jini a yayin gwagwarmayar kwatar ‘yancin kan Kamaru ya bude kundin ta’annatin mulkin mallaka ba tare da nuna da nuna damuwar da kasar ke bukata ba.
Wasikar da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya aike wa takwaransa na Kamaru ta tona asirin wannan sirrin da aka boye.. Photo: Others / Others
19 Agusta 2025

Faransa ta ci gaba da gudanar da ayyukanta na soji a Kamaru cikin rudanin gwamnati tsawon shekaru da dama.

Abin da gwamnatin Faransa ta kira "ayyukan tabbatar da zaman lafiya" a hakikanin gaskiya ayyuka ne na murkushe jama’a, inda aka kashe da dama daga cikin wadanda ke cikin masu fafutukar kwato 'yancin kai na Kamaru, yayin da aka garzaya da dubunnan daruruwa zuwa sansanonin tsare mutane.

Yanzu haka wata wasika da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya aike wa takwaransa na Kamaru ta tona asirin wannan sirrin da aka boye.

Wasikar, wacce aka bayyana a bainar jama'a a makon da ya gabata, ita ce karon farko da Faransa ta amince da amfani da "karfin tuwo don murkushe wa" a kasar da ke Tsakiyar Afirka.

Yayin da Macron bai nemi afuwa da bayar da hakuri ba kan wannan ta’asa, ikirarin da ya yi da bakinsa na nuni da yunkurin baya-bayan nan da Faransa ta yi na yin aminta da yadda ta yi mulkin mallaka, wanda ya zo daidai da ci gaba da rugujewar tasirinta a tsaffin kasashen Afirka, musamman a yankin Sahel.

"Abin da ke faruwa a yanzu bai isa ba. Har yanzu ba mu yi murna ba. Wannan ra'ayi ne na baki daga shugaba Macron, amma jama'a na son ganin karin bayani," wani masanin tarihin Kamaru, Dr Therence Atabong Njuafac, ya shaida wa TRT Afrika.

Ba a san girman munanan ayyukan Faransa a Kamaru ba a duk tsawon shekarun nan, har ma ga yawancin Faransawa. Labulen sirri ya kai ga mayar da kashe-kashe da bacewar mutane sun zama ruwan dare a wannan lokaci.

Waɗannan cikakkun bayanai sun fito fili ne watan Janairun bana a lokacin da masana tarihin Kamaru da Faransa suka fitar da wani rahoto a hukumance dangane da sabbin takardu da binciken adana kayan tarihi da suka shafi abubuwan da suka faru a shekarun 1950 da 1960.

"(Wasikar Macron) na nuna cewa abin da muke koyo game da tarihinmu na iya zama ba gaskiya ba kwata-kwata.

“An jirkita tarihin Kamaru har zuwa wani mataki. Mutane suna koyon wani abu da ba gaskiya ba ne," in ji Dokta Atabong, wanda aka kwatanta littafinsa na ‘Cry of Cameroonians’ a matsayin "wani mudubin mutanen da suka shiga tsaka mai wya da fatan samun mafita".

Yin shiru marar amfani

Labarin yadda aka yi wa Kamaru mulkin mallaka ya faro ne a karshen karni na 19 a lokacin da kasashen Turai da suka hada da Jamus da Birtaniya da Faransa suka yunƙura domin su mallaki yankunan Afirka.

Taron Berlin na 1884-1885 ya kawo sauyi, inda Jamus ta kafa ikonta a Kamaru.

Sai dai bayan da Jamus ta sha kaye a yakin duniya na farko, kasar Kamaru ta koma karkashin ikon kasashen Birtaniya da Faransa, inda Birtaniya ke rike da yankunan yammacin kasar, Faransa kuma ke rike da yankunan gabashi.

A ranar 1 ga watan Janairun 1960 ne Kamaru da ke karkashin mulkin mallakar Faransa ta samu 'yancin kai.

A shekara ta 1961, an hade yankunan Kamaru da ke karkashin ikon Birtaniya da Faransa. Ahmadou Ahidjo ne shugaban Kamaru na farko bayan samun 'yancin kan kasar.

Masana tarihi na kallon amincewar da Macron ya yi da ta'asar Faransa a Kamaru a matsayin wani lokaci mai cike da tarihi da zai iya baiwa 'yan Kamaru fahimtar tarihinsu na mulkin mallaka.

Ya zuwa lokacin da Kamaru ta samu 'yancin kai daga Faransa a watan Janairun 1960, sojojin Faransa sun kashe manyan jagororin kwatar 'yancin kai kamar Isaac Nyobè Pandjock, Ruben Um Nyobè, Félix-Roland Moumié, Paul Momo da Jérémie Ndéléné.

Yawancin abubuwan da suka faru a lokacin ko dai sun ɓace daga kundin tarihi na hukumomi ko kuma ba a shigar da su ba ma baki daya.

Manhajar makarantu a Kamaru ba ta da ambaton waɗannan batutuwa na gaskiya masu raɗaɗi sosai ba, shirun da mafi yawan manazarta suka danganta da haɗin kai tsakanin Faransa da ƙawayenta na cikin gwamnatin Kamaru bayan samun ‘yancin kan kasar.

"Yanzu muna da damar samun gaskiya. Alkawarin da Macron ya yi na bude ma'ajiyar bayanai na nufin masana tarihi, 'yan jarida, da iyalan wadanda aka kashe a halin yanzu za su iya zakulo shaidar aikata kashe-kashen jama'a da yawa, bacewar mutane da kashe-kashen manyan ‘yan siyasa, wanda ya baiwa Kamaru bayanan tarihi na karara," Dr Atabong ya fada wa TRT Afrika.

Kiraye-Kirayen biyan diyya

Yayin da sake rubuta tarihin samun ‘yancin kai na Kamaru bai zo farar daya ba, kin neman afuwa daga shugaban Faransa ko kuma ya yi kira da a biya diyya, na nufin har yanzu radadin na nan bai kau ba.

"Shi (Macron) bai tsara wani takamaiman tsari na shari'a ba. Yaya batun wuraren tuna wa da lamarin, tono gawawwaki daga kaburbura, ko ranakun tunawa a hukumance? Muna bukatar mu tuna waɗancan mutanen da suka gabace mu," in ji Dr Atabong.

Macron ya sanya sake daidaita dangantaka bayan mulkin mallaka da tsaffin kasashen Afirka da Faransa ta mulka a matsayin daya daga cikin abubuwan da ya sa a gaba a shugabancinsa, ko da yake har yanzu ana tantama kan sahihancin wadannan kokarin.

A shekarar da ta gabata, gwamnatinsa ta amince a karon farko cewa sojojin Faransa sun yi kisan kiyashi a kasar Senegal a shekarar 1944. Ya kuma amince da rawar da Faransa ta taka a kisan kiyashin da aka yi a Rwanda a shekarar 1994 da kuma yunkurin sasantawa da Aljeriya.

Masana dai na ganin cewa hare-haren da sojojin Faransa suka kai a Kamaru kafin samun 'yancin kai sun cancanci irin wannan amince wa.

"Muna son a kawar da nuna bambancin bude ma'ajiyar bayanai.....Kada su cire muhimman bayanai. Muna kuma son a nemi afuwar jama'a da ma dukkan wadanda abin ya shafa da zuriyarsu," in ji Atabong.

"Muna son matakan gyara. Za su iya zuwa ta hanyar bayar da tallafin karatu, samar da ababen more rayuwa, da ayyukan cigaba a yankunan da abin ya fi shafa.

“Muna bukatar tsarin sasantawa tsakanin kasashen biyu wanda zai mayar da hankali ga wadanda lamarin ya shafa."

Rikitacciyar dangantaka

A duk faɗin kasashe Afirka da Faransa ta yi wa mulkin mallaka, tsaffin ƙasashen da ta mulka na nuna tirjiya kan ci gaba da tasirin Faransa a kasashen da ma tsoma bakinya a cikin lamuransu na cikin gida.

Wasu daga cikin sabbin shugabannin kasashen na ganin wanzuwar Faransa, tare da da fifita yaren da mutanen ƙasashensu suka taso suna magana da rubutu da shi, a matsayin kalubale ga ‘yancin mulkin kansu.

Kamaru za ta iya zama fitacciyar kasa, aƙalla a hukumance. Yayin da ra'ayin jama'a ke juya wa Faransa baya, gwamnatin Yaoundé ta kasance kawa kuma aminiya. Shugaba Paul Biya mai shekaru 92 da ya kwashe kusan shekaru 43 yana mulki, a yanzu yana neman wa'adi na takwas a zaben watan Oktoba.

"Wataƙila talakawa, jama'a, su yi fushi da Faransa, amma gwamnati na tare da Faransa," in ji Atabong.

Wannan bambanci da ke tsakanin ra’ayin mafi yawan jama’a da manufofin gwamnati na bayyana bukatar adalci, biyan diyya da sulhu ingantacce wanda za a dade ba a tabbatar da su ba.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us