A lokacin wata tattaunawa a Fadar White House kan rikicin Ukraine a ranar Talata, Donald Trump ya gabatar da kansa a matsayin jagoran sulhu, yana ikirarin cewa ya fi son samar da dauwamammen zaman lafiya fiye da tsagaita wuta ta wucin gadi, tare da cewa ya kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe shida tun lokacin da ya hau mulki.
Amma idan aka yi duba sosai kan rikice-rikicen da Trump ya yi ikirari, akwai abubuwa masu rikitarwa.
Tarihin zaman lafiyar da yake ikirarin ya kawo gauraye yake da wasu abubuwan, inda wasu daga cikin rikice-rikicen da ya ce ya warware har yanzu suna da sauran ƙulli na tashin hankali ko kuma cikas ga al’amuran siyasa.
Gwamnatin Trump ta bayyana cewa ta taimaka wajen sasanta rikice-rikice tsakanin Isra’ila da Iran, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da Rwanda, Cambodia da Thailand, Indiya da Pakistan, Serbia da Kosovo, da kuma Masar da Habasha.
Amma abin da ake gani a zahiri, wadannan rikice-rikicen suna bayar da wata labari ne na daban.
Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo–Rwanda
Fada tsakanin sojojin gwamnati da ‘yan tawaye da Rwanda ke mara wa baya a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ya dauki tsawon shekaru, yana samun ƙarfi daga rikicin ƙabilanci da kuma takara kan albarkatu.
Duk da kokarin shiga tsakani na ƙasa da ƙasa, rikicin bai warware ba. A makon da ya gabata, ‘yan tawaye da Rwanda ke mara wa baya sun kasa cika wa’adin yarjejeniyar zaman lafiya a Doha, abin da ke nuna cewa har yanzu ba a samu zaman lafiya mai ɗorewa ba.
Gwamnatin Trump ta yi ikirarin taka rawa wajen kawo karshen rikicin, amma tashin hankalin da ke ci gaba ya saɓa wa duk wani zance na warware rikicin gaba daya.
Masar–Habasha
Haka nan, rikici tsakanin Masar da Habasha ya ta’allaka ne kan gina Madatsar Ruwa ta Renaissance ta Habasha a kan Kogin Nilu, wadda Masar ke ganin shirin zai iya rage yawan ruwan da take samu.
An yi jan ƙafa wajen tattaunawar sulhu kuma an kasa kammala su, lamarin da ya sa aka gaza warware rikicin tare da haifar da fargabar ƙarin rikici a nan gaba.
Trump da gwamnatinsa sun yi ikirarin shiga tsakani don ƙarfafa tattaunawa, amma babu wata yarjejeniya mai muhimmanci da aka cim ma.
Indiya–Pakistan
Rikici tsakanin Indiya da Pakistan kan Kashmir ya ta’azzara, inda bangarorin biyu ke musayar hare-hare da zarge-zarge. A watan Mayu, tashin hankali ya ƙara tsananta.
Gwamnatin Trump ta yi ikirarin shiga tsakani don cim ma tsagaita wuta, tana gabatar da hakan a matsayin nasarar diflomasiyya.
A ranar 10 ga Mayu, bayan rikici tsakanin Indiya da Pakistan, Trump ya sanar cewa: “Bayan shafe dare ana tattaunawa mai tsawo sakamakon shiga tsakanin da Amurka ta yi, ina farin cikin sanar da cewa Indiya da Pakistan sun amince da tsagaita wuta nan take. Ina taya ƙasashen biyu murna kan amfani da hankali da basira.”
Sai dai gwamnatin Indiya ta musanta cewa Trump ya taka wata muhimmiyar rawa wajen dakatar da rikicin, tana mai jaddada cewa abin da ake kira sulhu da Amurka ta shiga tsakani ya fi kama da alama kawai.
Pakistan, duk da haka, ba ta ƙalubalanci ikirarin Trump ba inda har ma ta gabatar da sunansa don samun lambar yabo ta Nobel kan rawar da ya taka wajen kawo ƙarshen rikicin.
Serbia–Kosovo
Dangantaka tsakanin Serbia da Kosovo ta kasance mai cike da tashin hankali tun bayan da Kosovo ta samu ‘yancin kai a shekarar 2008.
Duk da cewa Trump ya dauki kansa a matsayin wanda ya hana yaki tsakanin kasashen biyu, Serbia ta musanta cewa tana da wani shiri na yaki, tana nuna cewa rikicin bai yi ta’azzarar da ake ikirari ya yi ba.
Jami’an Amurka sun yaba da shiga tsakani na diflomasiyya, amma rashin wani rikici na zahiri ya sanya alamar tambaya a kan ikirarin Trump na zama mai sulhu.
Iran–Isra’ila
Tashin hankali mai tsawo tsakanin Iran da Isra’ila ya haɗa da barazana kan ƙarfin nukiliya, da samun tasiri a yankin, da kuma ayyukan soja.
Amurka ta kai hare-hare da bama-baman ƙarƙashin ƙasa kan sansanonin soja da na nukiliya kafin ta matsa wa Tehran ta amince da tsagaita wuta, wanda ya kara rikitar da labarin Trump a matsayin mai sulhu.
Kan Isra’ila da Iran, Trump ya rubuta cewa, “An amince gaba daya tsakanin Isra’ila da Iran cewa za a samu cikakkiyar tsagaita wuta.”
Duk da ikirarin Trump na warware rikicin, wadannan matakan na tashin hankali sun nuna cewa “yarjejeniyoyin zaman lafiya” sun fi kama da matsa lamba fiye da warware rikice-rikice.
Cambodia–Thailand
A karshen watan Yulin 2025, rikice-rikicen kan iyaka tsakanin Cambodia da Thailand sun yi sanadin kashe mutane da dama kuma sun raba dubban mutane da gidajensu.
Bangarorin biyu sun zargi juna da tashin hankali, wanda ya hada da fashewar nakiyoyi da musayar wuta.
Gwamnatin Trump ta yi ikirarin shiga tsakani na diflomasiyya don taimakawa wajen dakatar da rikicin. Malaysia da China su ma sun taimaka wajen shiga tsakani.
Trump ya bayyana kokarin dakatar da rikicin kwanaki uku na kan iyaka tsakanin Thailand da Cambodia: “Tattaunawar da Cambodia ta ƙare, amma ana sa ran sake kira kan dakatar da yaƙi da tsagaita wuta bisa abin da Thailand za ta ce. Ina kokarin sauƙaƙa wani yanayi mai rikitarwa!”
An sanar da tsagaita wuta a ranar 28 ga Yuli, amma rahotannin karya dokar tsagaita wuta da ci gaba da tashin hankali sun nuna cewa yarjejeniyar tana da rauni.
Zaman lafiya fiye da tsagaita wuta?
Duk da cewa yanzu Trump yana cewa yana guje wa tsagaita wuta don fifita yarjejeniyoyin zaman lafiya masu fadi, maganganunsa suna nuna wani labari daban.
MSNBC, tashar labarai ta talabijin ta Amurka, ta bayyana yadda Trump ya maimaita kiran tsagaita wuta a Ukraine a makonnin da suka gabata kafin ganawarsa da Putin da Zelenskyy.
Duk da haka, a Alaska makon da ya gabata, Trump ya gana da Putin, wanda ya bukaci Ukraine ta miƙa yankuna a kudu maso gabas kafin a iya tattauna wani tsagaita wuta.
Zuwa taron da aka yi da shugabannin Turai a ranar Litinin, Trump ya ce ba ya neman tsagaita wuta.
“Idan ka duba yarjejeniyoyi guda shida da na warware a wannan shekarar, duk suna cikin yaki. Ban nemi wata tsagaita wuta ba,” Trump ya fada wa Zelenskyy, inda ya ƙara da cewa, “Ba na tsammanin kuna bukatar tsagaita wuta.”
Ko da yake yana daukar kansa a matsayin mai tsara yarjejeniyoyin zaman lafiya da dama, mafi yawan rikice-rikicen ba a warware su ba.
Kuma a Gaza, Isra’ila tana ci gaba da yakin kisan kare dangi kan Falasdinawa tare da cikakken goyon bayan Trump.