SIYASA
1 minti karatu
INEC za ta fara rajistar masu zaɓe a faɗin Nijeriya ranar 18 ga Agustan 2025
Hukumar ta ce za a buɗe rajistar masu kaɗa ƙuri’a ta intanet a ranar 18 ga watan Agusta ta hanyar tasharta, cvr.inecnigeria.org.
INEC za ta fara rajistar masu zaɓe a faɗin Nijeriya ranar 18 ga Agustan 2025
INEC za ta fara rajistar masu zaɓe a faɗin Nijeriya ranar 18 ga Agustan 2025 / Reuters
1 Agusta 2025

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya ta ce za a fara gudanar da rajistar masu kaɗa ƙuri’a na shekarar 2025 a duk faɗin ƙasar a ranar 18 ga watan Agusta.

INEC ta bayyana hakan ne a shafinta na X ranar Juma'a.

Hukumar ta ce za a buɗe rajistar masu kaɗa ƙuri’a ta intanet a ranar 18 ga watan Agusta ta hanyar tasharta, cvr.inecnigeria.org.

Ya bayyana cewa za a fara rajistar mutanen nan da mako guda, ranar 25 ga watan Agusta.

A cewarta, za a gudanar da wannan aiki a duk fadin kasar a dukkan ofisoshin kananan hukumomin da kuma wuraren da aka keɓe.

INEC ta ce za a gudanar da aikin ne daga ranar Litinin zuwa Juma'a, daga karfe 9 na safe zuwa karfe 3 na rana.

"Kuri'unku sun ta’allaƙa ne da yin rajistarku. Ka da ku rasa damarku ta yin rajista," in ji shi.

A bisa ƙa’ida ‘yan shekara 18 zuwa sama ne kawai ke da izinin yin zaɓe a Nijeriya.

A shekarar 2027 ne za a sake yin manyan zaɓuka a Nijeriya.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us