A wani sabon mataki na magance ta’addancin siyasa da tashin hankali tsakanin matasa, Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon shiri mai suna “Safe Corridor” na yin afuwa da farfaɗo da rayuwar matasan da suka tuba daga munanan ɗabi’u waɗanda suka haɗa da harkar daba a jihar.
Gwamna jihar Abba Kabir Yusuf ya fito da wannan tsarin ne da nufi rage barazanar da ƙungiyoyin matasa masu tayar da rikici ke yi.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan daban suka addabi jama’ar jihar musamman da ƙwacen wayoyi da kuma kashe waɗanda suke ƙwace wa wayoyin a wasu lokutan.
Kwamishinan Watsa Labarai na Kano Ibrahim Abdullahi-Waiya ya ce gwamnan ya nuna matuƙar damuwa dangane da yadda harkar daba ke ƙara ƙaruwa a jihar inda ya ce lamarin na ƙara ƙazanta kuma yana ɓata wa jihar suna.
A shirye-shiryen gwamnatin na afuwa, tuni aka tantance matasa 718, yayin da wasu 960 ke jiran tantancewa daga rundunar ’yan sanda kafin a haɗa su cikin shirin.
Tsarin tantancewar ya haɗa da binciken tsaro daga ’yan sanda, gwajin miyagun ƙwayoyi daga hukumar NDLEA, sannan daga nan za a shiga matakin gyara hali da sake haɗa su cikin al’umma.
Me waɗanda suka tuba za su amfana da shi?
Babban tagomashin da waɗanda suka tuba za su samu daga gwamnatin jihar shi ne afuwa.
Wannan na nufin za a yafe musu duka laifuffukansu sannan kuma a ba su dama domin rayuwa a matsayin ‘yan ƙasa masu bin doka.
Gwamnati ta kuma yi alƙawarin samar da ayyukan yi, sana’o’in dogaro da kai da kuma tallafin ga tubabbun domin ƙarfafa musu gwiwa wajen sake gina rayuwarsu.
Rawar da masu ruwa da tsaki za su taka
Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori ya yaba wa shirin, ya kuma roƙi sauran masu laifi da su mika wuya, yana mai cewa wannan dama ce ta fara sabuwar rayuwa da kuma dawowa a cikin al’umma
Kwamandan Hukumar Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Daurawa ya buƙaci matasan da suka shiga shirin su kasance jakadun zaman lafiya, su kuma shawarci sauran abokan su da su tuba.
Ya kuma nuna yiwuwar yi wa waɗanda suka sauya halayen nasu auren gata.
Sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin farar hula da sauran hukumomin tsaro za su sa ido wajen aiwatar da shirin domin tabbatar da gaskiya da bin doka.
Girman matsalar daba da ƙwacen waya a Kano
Matsalar daba da ƙwacen waya ta kasance wani muhimmin lamari wanda ke buƙatar daƙile shi cikin gaggawa a Kano.
Sakamakon yadda lamarin ya ƙazanta, babu ranar da za ta zo ta wuce ba tare da an samu rahoton faɗan daba, ko na ƙwacen waya ba a sassan jihar daban-daban, abin da ke sanya fargaba da tsoro a zuƙatan al’ummar jihar.
Saboda tsananin yadda abin ya yi muni da yadda ake yawan samun faruwar matsalar, akwai hanyoyi da unguwannin Kano da jama’a suke ƙaurace musu musamman idan dare ya yi.
Jama’ar jihar sun jima suna kokawa kan wannan matsalar inda har a kwanakin mata a unguwannin Zango da Korar Mata sun fita sun yi zanga-zanga saboda yadda ake neman hana su sakat su da yaransu.