Yara goma da aka sace a yankin arewacin Kamaru mai fama da rikici a makon da ya gabata sun samu 'yanci a wani aikin ceto, amma wani daga cikin waɗanda aka sace ya rasa ransa, a cewar gwamnan yankin.
Hukumomin Kamaru ba su yi wani tsokaci ba tun bayan da aka sace yaran yayin da suke tafiya a cikin mota daga Kousseri zuwa Maroua, sannan aka kai su zuwa Najeriya ta iyaka.
Amma gwamnan yankin Arewa Mai Nisa, Midjiyawa Bakari, ya bayyana a cikin wani bidiyo da aka wallafa a kafar sada zumunta a ranar Alhamis cewa sojojin rundunar Kamaru tare da hadin gwiwar sojojin Nijeriya da Chadi sun ceto yara goma.
"Abin takaici, ɗaya daga cikinsu ya rasa ransa," in ji shi, ba tare da bayar da karin bayani ba.
An kama mutane
A jumalla, kimanin mutane 15 aka sace, in ji Bakari, ba tare da bayar da karin bayani kan wadanda aka sako ba. Ya kara da cewa an kama mutane 50.
Gwamnan bai yi tsokaci kan yadda aka yi satar ba ko kuma ko wadanda suka aikata laifin suna da alaka da kungiyar ta'addanci ta Boko Haram ba, kamar yadda kafafen yada labarai na Kamaru suka ruwaito.
Tun daga shekarar 2009, Boko Haram ta addabi yankin arewa maso gabashin Nijeriya, wanda ya shafi kasashe makwabta, ciki har da arewacin Kamaru.
Kungiyar ta yi amfani da satar mutane a matsayin wani bangare na dabararta, musamman sace 'yan mata kusan 300 daga makarantar su a garin Chibok na Nijeriya a shekarar 2014.
Fushin jama'a
Satar yaran a Kamaru ta jawo fushin jama'a inda suka zargi gwamnati da rashin daukar mataki.
Iyalan wadanda aka sace sun yi Allah wadai da rashin bayani daga gwamnati, yayin da aka kaddamar da wani gangamin tara kudi don ganin an sako wadanda aka sace.
Gwamnan Arewa Mai Nisa ya ce an tura jami'an tsaro "tsawon mako guda" don "bincika yankin" da kuma tilasta "'yan ta'adda" su sako wadanda suka sace.
Baya ga satar mutane, fararen hula a yankin suna fuskantar barazanar hare-hare daga Boko Haram da kuma ISWAP, wata kungiyar ta'addanci da ke da alaka da Daesh. An samu rahoton hare-hare 246 a shekarar 2023, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla fararen hula 169.