NIJERIYA
1 minti karatu
Abdullahi Bashir Haske: EFCC na neman surukin Atiku Abubakar ruwa-a-jallo
Abdullahi Bashir Haske ɗan kasuwa ne a man fetur na Nijeriya, kuma suruki ga tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar.
Abdullahi Bashir Haske: EFCC na neman surukin Atiku Abubakar ruwa-a-jallo
Bashir Haske / EFCC
11 awanni baya

Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta yi shelar neman Abdullahi Bashir Haske, surukin tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar, ruwa-a-jallo.

Wata sanarwar da EFCC ta wallafa a shafukanta na sada zumunta ranar Alhamis da maraice ta ce hukumar tana neman mutumin ne bisa zargin halatta kuɗin haram da haɗa baki domin aikata laifuka.

Sanarwar da shugaban fannin hulɗa da jama’a na hukumar, Dele Oyewale, ya sanya wa hannu, ta ce Abdullahi Bashir Haske mai shekara 38, an san shi ne da zama a gida mai lamba ta 6 a kan titin Mosley a unguwar Ikoyi da ke birnin Legas.

Abdullahi Bashir Haske dai ɗan kasuwa ne da ke fannin man fetur a Nijeriya, kuma suruki ne ga tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar.

Kawo yanzu dai ba a ji komai daga ɗan kasuwar da hukumar take nema ba.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us