NIJERIYA
2 minti karatu
Ibrahim Bakura: Rundunar Sojin Nijar ta ce ta kashe wani jigo a Boko Haram
Taƙaitacciyar sanarwar da rundunar sojin ta Jamhuriyar Nijar ta fitar ta bayyana harin sama na sojin a matsayin wanda ba a saba kai irinsa ba.
Ibrahim Bakura: Rundunar Sojin Nijar ta ce ta kashe wani jigo a Boko Haram
Rahotanni sun ce Ibrahim Bakura ya jagoranci Boko Haram bayan mutuwar Abubakar Shekau / Getty
22 Agusta 2025

Rundunar sojin Nijar ta ce ta yi nasarar kashe wani ƙasurgumin ɗan Boko Haram Ibrahim Bakura, wanda ake kira Abu Umaima.

Wata sanarwar da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Alhamis ta ce dakarunta sun yi nasarar kashe ɗan Boko Haram ɗin ne a wani hari na musamman da ta kai tsibirin Shilawa a yankin Tafkin Chadi da safiyar ranar 15 ga watan Agusta.

Taƙaitacciyar sanarwar da rundunar sojin ta Jamhuriyar Nijar ta fitar ta bayyana harin sama na sojin a matsayin wanda ba a saba kai irinsa ba.

Rahotanni sun nuna cewa Ibrahim Bakura ya jagoranci wani ɓangare na Boko Haram bayan mutuwar Abubakar Shekau, kuma ya tafi yankin Tafkin Chadi da ke ɓangaren Jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar da mayaƙansa.

Kazalika Bakura, wanda asalin sunansa Ibrahim Mahamadu, mai shekara 40 ɗan asalin Nijeriya ne, kamar yadda wasu rahotanni suka ambato sojin Nijar na cewa.

Rikicin Boko Haram da aka fara tun shekarar 2009 a Nijeriya dai ya kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu.

Kuma bayan an fara shi a Nijeriya ne rikicin ya fantsama ƙasar Nijar inda ‘yan ta’addan suka fara kai hare-hare yankin Tafkin Chadi da ke Bosso a shekarar 2015.

 

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us