Ana tafka muhawara kan batun ƙarin albashi ga masu riƙe da mukaman siyasa a Nijeriya
NIJERIYA
3 minti karatu
Ana tafka muhawara kan batun ƙarin albashi ga masu riƙe da mukaman siyasa a NijeriyaTuni ƙungiyar ƙwadago da wasu jam'iyyun siyasa a Nijeriya suka fara sukar wannan shirin bayan Shugaban Hukumar raba arzikin ƙasa ta Nijeriya (RMAFC) Mohammmed Shehu ya bayar da shawarar ƙarin albashin.
Shugaban hukumar RMAFC ya ce bai kamata a ce ana biyan shugaban Nijeriya naira miliyan daya da rabi ba a wata ba / Nigeria Presidency
21 Agusta 2025

Ana ci gaba da tafka muhawa kan batun karin albashi ga masu riƙe da mukaman siyasa a Nijeriya tun bayan da Shugaban Hukumar raba arzikin ƙasa ta Nijeriya (RMAFC) Mohammmed Shehu ya yi ikirarin cewa albashin da masu rike da mukaman siyasa ke karba bai taka kara ya karya ba, a daidai lokacin ake fama da matsin tattalin arziki a ƙasar, kamar yadda ya bayyana yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja a farkon makon nan.

Shugaban hukumar ya ce a halin da ake ciki Shugaba Bola Tinubu na karbar naira miliyan 1.5 ne a kowanne wata a matsayin albashi, yayin da abin da ministoci ke karɓa bai kai naira miliyan ɗaya ba. Sannan ya ce tun shekarar 2008 ake amfani da wannan tsari kuma har yanzu bai canja ba.

Shugaban hukumar ya ce bai kamata a ce ana biyan shugaban Nijeriya naira miliyan daya da rabi ba a wata a kasa mai yawan jama’ar da suka kai mutum miliyan 200.

Sai dai Kungiyar Kwadago a Nijeriya (NLC) ta soki shirin hukumar raba arziƙin ƙasar na yi wa masu riƙe da mukaman siyasa karin albashi, inda kungiyar ta bayyana matakin da wani yunkurin yin biris da yadda ake ci gaba da samun wagegen gibi tsakanin manyan ma’aikatan gwamnati da kanana, sannan NLC ta ce dama can alawus-alawus din da ake ba manyan ma’aikata ya kara girman gibin da ake da shi.

Ita ma sabuwar jam’iyyar hadakar ’yan adawa a kasar ADC ta bayyana damuwa game da shirin kara albashin masu rike da mukaman siyasa a kasar.

Jam’iyyar ta ce ’yan Nijeriya ya kamata a kara wa albashi, amma ba ’yan siyasa ba. Sannan ADC ta ce, la’akari da lokacin da ake kokarin yi wa masu rike da mukaman siyasa kari, wata manuniya ce da ke nuna yadda gwamnatin kasar ba ta fahimci halin da ’yan kasa suke ciki ba, kamar yadda Sakataren Yada Labaran Jam’iyyar na Kasa Mallam Bolaji Abdullahi ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Sannan wasu jaridun Nijeriya sun ruwaito cewa jagoran jam’iyyar adawa ta NNPP a shiyyar Kudu Maso Yammaci kasar Olufemi Ajadi Oguntoyinbo ya yi Allah-wadai da shirin karin albashin manyan ’yan siyasar kasar.

Mr Ajadi ya ce miliyoyin ’yan kasar suna cikin mayuwacin hali a daidai lokacin da ake ci gaba da samun hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi a kasar. Sannan ya ce kamata ya yi masu rike da mukaman siyasa su rage wa kansu albashi kuma kada su nemi kari a wannan lokaci.

Kazalika ita ma jam’iyyar adawa ta PDP ba ta goyi bayan karin ba, inda ta bayyana cewa matakin rashin nuna tausayi ne ga matsanancin halin matsin tattalin arzikin da ’yan Nijeriya suke ciki, kamar yadda Mataimakin Shugaban Matasa a Jam’iyyar PDP Timothy Osadolor ya bayyana wa manema labarai a Abuja.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us