Ƙasar Ethiopia ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya tare da wani reshe na Rukunin Kamfanonin Dangote na Nijeriya don gina wata masana'antar samar da takin zamani mai darajar dala biliyan 2.5, in ji Firaminista Abiy Ahmed a ranar Alhamis a wani saƙo da ya wallafa a shafin X.
Abiy ya bayyana cewa yarjejeniyar da aka ƙulla tare da Dangote Group na attajirin Afirka Aliko Dangote, za ta sanya Ethiopia cikin manyan masu samar da takin zamani a duniya.
Masana'antar, wadda za a fara gina ta nan ba da jimawa ba, tana da damar samar da har zuwa tan miliyan uku na takin zamani a kowace shekara, in ji Firaministan.
A halin yanzu, Afirka tana shigo da fiye da tan miliyan shida na takin zamani a kowace shekara, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
‘Tabbacin wadatar kayayyaki’
“Wannan aikin zai samar da ayyukan yi a cikin gida, ya tabbatar da wadatar takin zamani ga manomanmu da suka dade suna fuskantar kalubale, kuma zai zama mataki mai muhimmanci a kokarinmu na samun ikon cin gashin kai wajen samar da abinci,” in ji Abiy.
A watan Yuni, attajirin ɗan kasuwar daga Nijeriya ya bayyana cewa Afirka za ta zama mai wadatar takin zamani cikin watanni 40 bisa tsarin fadada masana'antarsa ta dala biliyan 2.5 da ke Lagos, cibiyar kasuwancin Nijeriya.