A daidai lokacin da makamashi ke ƙara tsada a Nijeriya, ‘yan ƙasar sun kashe kimanin Naira tiriliyan 1.3 wajen man fetur domin amfani da shi a motocinsu da kuma janareto domin samun wutar lantarki a watan Yuni.
Sannan kuma amfani da fetur a fadin ƙasar ya kai lita biliyan 1.44, a cewar sabbin bayanan da Hukumar kula da harkokin sarrafawa, tacewa da sufurin man fetur ta Nijeriya, NMDPRA ta fitar.
‘Yan Najeriya na amfani da fetur fiye da kowanne irin mai, kuma saboda rashin wadatacciyar wutar lantarki daga gwamnati, mafi yawan al’umma suna dogaro da fetur wajen samar da wuta.
Bayan cire tallafin fetur shekaru biyu da suka wuce, kudin da ‘yan Nijeriya ke kashewa wajen sayen mai ya kai matakin da ba a zata ba, in ji rahoton jaridar Punch.
A bisa bayanan NMDPRA, jihohin Legas, Ogun da Babban Birnin Tarayya (Abuja) ne suka fi shan fetur a watan Yuni.
Rahoton rarraba fetur na NMDPRA na watan ya nuna cewa jumillar lita biliyan 1.44 na fetur aka aika jihohi.
Idan aka ɗauki farashi matsakaici na Naira 900 kan kowace lita, hakan ya kai kimanin Naira tiriliyan 1.3.
Daga cikin lita biliyan 1.44 da aka aika, Legas ta shanye lita miliyan 205.7, wanda ya kai kimanin Naira biliyan 185.1.
Ogun ta biyo baya da lita miliyan 88.7 da darajar fetur ɗin ya kai Naira biliyan 79.8, yayin da Abuja ta samu lita miliyan 77.5 da darajarta ta kai Naira biliyan 69.8. Oyo, wadda ke kusa da Legas, ta samu lita miliyan 72.8 da darajarta ta kai Naira biliyan 65.5.
Jihohin da suka fi karɓar fetur maras yawa sun haɗa da Jigawa inda ta karbi lita miliyan 9.4 kimanin Naira biliyan 8.5. Sai Ebonyi inda ta karɓi lita miliyan 10.5 wanda kuɗinta ya kai Naira biliyan 9.5.
Yobe da lita miliyan 11.7 wanda kuɗinta ya kai Naira biliyan 10.5b da kuma Bayelsa inda ta samu lita miliyan 11.9 inda kuɗinta ya kai Naira biliyan 10.7.
A matakin yanki, yankin kudu maso yamma ne ya fi amfani da fetur da jimillar lita miliyan 452.9 da kuɗinta ya kai Naira biliyan 407.7.
Bayan Legas, Ogun da Oyo, Osun ta samu lita miliyan 35.5 (N31.9bn), Ondo lita miliyan 35.1 (N31.5bn), da Ekiti lita miliyan 15.3 (N13.7bn).
Yankin Tsakiyar Arewacin Nijeriya ya zo na biyu da lita miliyan 247.4 da darajarta ya kai Naira biliyan 222.4.
Abuja ita ce kan gaba da lita miliyan 77.5 wanda ta kai Naira biliyan 69.8, sai Neja ta samu lita miliyan 40.7 da kuɗinta ya kai Naira biliyan 36.6.
Sai Kwara da ta samu lita miliyan 34.8 da kuɗinta ya kai Naira biliyan 31.3 sai Benue ta samu lita miliyan 25.7 da kuɗinta ya kai Naira biliyan 23.1, sai Nasarawa da lita miliyan 25.1 inda kuɗinta ya kai Naira biliyan 22.6.
Kogi da lita miliyan 24.1 da kuɗinta ya kai Naira biliyan 21.7, sai Filato da lita miliyan 19.4 da kuɗinta ya kai Naira biliyan 17.5.
Arewa maso yamma ta shanye lita miliyan 230 da darajarta ta kai Naira biliyan 207. Kano ta jagoranci yankin da Naira biliyan 61.4 sai Kaduna Naira biliyan 38.8 da Sokoto Naira biliyan 33.3.
Kebbi ta kashe Naira biliyan 27.3 sai Katsina Naira biliyan 22.3 sai Zamfara Naira biliyan 15.3, yayin da Jigawa ta fi ƙaranci da Naira biliyan 8.5.
A kudu maso kudu, kuɗaɗen da aka kashe sun kai Naira biliyan 202.9 kan lita miliyan 224.9. Delta ita ce kan gaba a yankin da Naira biliyan 61.6, sai Jihar Ribas ta kashe Naira biliyan 40.1, sai Edo Naira biliyan 38.
Haka kuma Akwa Ibom ta kashe Naira biliyan 30.4 da Cross River Naira biliyan 20.7, yayin da Bayelsa ke daga cikin mafi ƙanƙanta da N10.7bn.
Bayanan NMDPRA sun nuna cewa arewa maso gabas ta shanye lita miliyan 152.8 da darajarta ta kai Naira biliyan 137.5.
Adamawa ita ce kan gaba a yankin da Naira biliyan 51.2, sai Bauchi da Naira biliyan 27.9 inda Gombe da Borno suka shanye Naira biliyan 17.3 da Naira biliyan 17 sai Taraba Naira biliyan 13.6, yayin da Yobe ta fi ƙaranci da Naira biliyan 10.5.
Kudu maso gabas ce ta fi ƙarancin shan mai a fadin ƙasar da lita miliyan 132.7 da kuɗinta ya kai Naira biliyan 119.6.
Anambra ta ce kan gaba a yankin da lita miliyan 40.5 da kuɗinta ya kai Naira biliyan 36.5, sai Imo lita da miliyan 30.6 da kuɗinta ya kai Naira biliyan 27.6.
Sai Enugu ta shanye lita miliyan 27.4 inda kuɗin ya kai Naira biliyan 24.7, Abia ta shanye lita miliyan 23.7 inda kuɗinta ya kai Naira biliyan 21.3 sai Ebonyi inda ta shanye lita miliyan 10.5 da kuɗinta ya kai Naira biliyan 9.5.