Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar da wata sanarwa mai lamba: 183, a ranar 9 ga Satumban 2025, “Dangane da Harin Isra’ila kan Doha, Babban Birnin Qatar”.
“Muna Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan tawagar tattaunawar Hamas a Doha, babban birnin Qatar,” sanarwar ta fara da cewa.
Ma’aikatar ta nuna cewa ayyukan Isra’ila suna da rikitarwa; a gefe guda tana nuna kamar tana son tattaunawa don kawo karshen yakin Gaza da dawo da mutanen Isra’ila da aka yi garkuwa da su, amma a gefe guda tana ƙara tayar da tarzoma har ma a wasu yankunan da ba na Falasdinu.
“Kai hari kan tawagar tattaunawar Hamas yayin da ake ci gaba da tattaunawar tsagaita wuta yana nuna cewa Isra’ila tana son ci gaba da yaƙi, ba zaman lafiya take nema ba.”
Ma’aikatar ta ce Isra’ila tana ƙara samun sabbin abokan gaba ta hanyar kai hare-hare ba tare da wani dalili ba: “Da wannan hari, Qatar, wadda ta shiga tsakani wajen tattaunawar tsagaita wuta, ta shiga jerin kasashen da Isra’ila ke kai wa hari a yankin.”
“Wannan hujja ce a fili kan manufofin fadada yankin da Isra’ila ke yi da kuma daukar ta’addanci a matsayin manufofin gwamnatinta.”
Ma’aikatar ta sake jaddada goyon bayanta ga Qatar wadda ta kasance mai shiga tsakani a yaƙin Gaza, tana daukar nauyin tattaunawa don kawo karshen wahalhalun da al’ummar Falasdinu ke sha.
“Muna tare da Qatar kan wannan mummunan hari da ya nufi keta ikon mallaka da tsaronta. Muna sake kira ga al’ummar duniya da su matsa wa Isra’ila lamba don kawo karshen hare-haren da take ci gaba da kaiwa a Falasdinu da yankin.”