DUNIYA
10 minti karatu
Isra'ila, Turkiyya da ƙalubalen zaman lafiya a Syria bayan yaƙi
Isra'ila na da manufar rarraba kasar Syria, yayin da rawar da Turkiyya ke taka wa wadda ke kara habaka za ta taimaka wajen samar da zaman lafiya da karfafa karfin ikon Damascus.
Isra'ila, Turkiyya da ƙalubalen zaman lafiya a Syria bayan yaƙi
Sojojin Syria sun daga tutar kasar a Damascus, suna nuna tirjiya a yayin da Isra'ila ke ta kai hare-hare ta sama. / AP
9 Satumba 2025

Daga Charlse Mbolu

Siriya na farfadowa daga yakin basasa na fiye da shekaru goma; makomarta na cikin tsananin rashin tabbas. Rikicin yanki da tsoma bakin kasashen waje na ci gaba da yin tasiri wajen farfadowar kasar.

Hanyoyi guda uku sun fito fili: hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa da manufofin tarwatsawa, shirun da kasashen duniya suka yi, da rawar da Turkiyya ta taka a matsayin garanton yuwuwar tabbatar da kwanciyar hankali ne ke tattare da wannan rikitaccen yanayi.

Wannan na kawo tambayoyi masu mahimmanci. Menene ainihin manufar Isra'ila a Syria? Me ya sa duniya ta yi shiru tsit bayan tsananta kai hare-hare sakamakon yakin Gaza?

Shin shigar da Syria cikin Yarjejeniyar Abraham zai iya gamsar da damuwar tsaro da Isra'ila ke da ita? Kuma a ina ne Turkiyya za ta sanya kanta a cikin wannan yanayi mai sauya wa?

Mummunan wasan Isra’ila a Syria

Abu na farko da za ta yi shi ne gangamin Isra'ila don ci gaba da wargaza Syria. Baya ga kisan kiyashin da ake ci gaba da yi a Gaza, Tel Aviv na kuma kai hare-hare da yunkurin mamaye wasu kasashe makwabta.

Bayan 7 ga Oktoba, saboda yanayin tsaro da ta shiga, Isra'ila ta fada cikin wani yanayi na yaƙe-yaƙe marasa iyaka don sake aikata ta’annatin da ta saba yi.

A lokacin da hakan ke faru wa, wannan ita ce hanya daya tilo da ke hannun firaminista Benjamin Netanyahu don ci gaba da rike gwamnatin masu tsaurin ra’ayi.

A batun Syria kuma, Isra'ila tana aiki a matsayin ci gaba da dabbaka manufofinta na baya. Abin da take ƙoƙarin yi a Syria ya samo asali ne daga ƙa'idar da aka fi sani da ƙawance na yanki, wanda ke nufin haɗa kai da tsiraru da ƙasashen da ke kewaye da su don raunana ƙasashen Larabawa masu adawa da juna a yankin.

Taimakon siyasa da na soja da aka baiwa kungiyoyin Druze karkashin jagorancin Hikmat al-Hijri, ya samu ne daga wannan tsarin.

Druze ‘ƴan tsiraru ne amma masu magana da Larabci a Syria, sun kai su kusan miliyan kuma suna da ƙarfi da zama a Suwaida kusa da kan iyakokin Isra'ila da Jordan. 

A watan Yuli,  arangama ta barke tsakanin Larabawa mazauna kauye da kungiyoyin Druze a yankin. A lokacin da Damascus ta tura dakaru domin dawo da zaman lafiya, Isra'ila ta kai hare-hare ta sama kan dakarun gwamnati, tana mai ikirarin kare tsiraru daga kisan kiyashi.

Lamarin ya nuna yadda Tel Aviv ke amfani da matsalolin cikin gida na Syria, musamman a tsakanin Druze, don dakile kokarin baya bayan nan na sake hade kan Syria waje guda.

Wannan ya yi daidai da babban lissafin Isra'ila. A mahangar Isra'ila, daidaituwar Syria bayan Assad, da tsayawa kan halaccin jama'a, farfado da tattalin arziki, da kuma maido da ikon yankin, zai zama lamari mafi muni gare ta.

Damascus mai karfi na iya hana Isra'ila 'yancin gudanar da hare-haren wuce gona da iri, da mika makamai ga wakilan da ta ga dama, da kuma sarrafa masu yi mata aiki da ke kasar.

Saboda haka, Isra'ila take ta yin ƙoƙarin tabbatar da cewa Syria ta zama ƙasa mai rauni, wanda ke fama da adawar cikin gida, ‘yan bindiga na sa kai da kuma tsoma bakin kasashen waje.

Wannan ya bayyana a goyon bayan Isra'ila ke bai wa ƙungiyoyin Druze ko kuma amincewa da yunkurin 'yan ta'addar PKK/YPG, a matsayin wata hanya ta lalata ikon gwamnatin tsakiya ta Syria.

Wani abu da ya ci karo da hakan shi ne yadda Netanyahu ya sha bayyana cewa Isra'ila ba za ta ƙyale Syria ta "zama wata Lebanon ba."

Amma duk da haka, a aikace, manufofin Isra'ila suna matsawa Syria zuwa daidai da tsarin na Labanon na rarrabuwar kawuna ta hanyar hana sojojin Syria sake shiga yankunan kudanci, da kai hare-hare ta sama, da samar da yanayi na yawaitar sojoji da mayaka.

Abin da ke damun Isra'ila musamman shi ne nasarar rawar da Ankara ke takawa a Syria.

A lokacin yakin basasa, Turkiyya ta dauki nauyin kashe kudade don karbar miliyoyin 'yan gudun hijira tare da tsaya wa a matsayin babbar mai goyon bayan 'yan adawar Syria na lokacin da suke adawa da gwamnatin Assad.

Yanzu, a cikin yanayi na bayan yakin basasa, Ankara tana sake daidaita kanta. Yunkurin kulla alaka tsakanin Turkiyya da Syria, musamman idan aka hada tare da rage goyon bayan Amurka ga PKK/YPG, zai iya karfafa ikon Damascus a lokaci guda, da fadada tasirin Turkiyya a yankin, da kuma dakile ikon Isra'ila na yin aiki ba tare da izini ba a duk fadin Syria.

Don haka, batun tsaron Isra'ila na ɓoye abin da ke cikin ainihin dabarar ci gaba da jin daɗin tsoma baki a cikin ƙasashen Larabawa da ke makwabtaka da ita, jin daɗi da ke fuskantar barazana daga samun karfin ikon Turkiyya a yankin.

Aikin da ba zai yiwu ba: Yarjeniyoyin Abraham

Ta hanyar amfani da ƙarfin soji a matsayin kayan aikinta na yau da kullun, Tel Aviv na fuskantar hatsarin kulle Siyria a cikin yanayin rarrabuwar kawuna da kuma ƙara hatsarin faɗaɗar rikici a yankin. A lokaci guda kuma, kasashen duniya sun mayar da yadda Isra'ila ke keta hurumin kasar Syria ba komai ba.

Duk da wanzuwar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kan iyakar Syria da Isra'ila da ke iyakar Golan a karkashin yarjejeniyar raba iyaka ta 1974, Isra'ila ta yi amfani da damar hakan a watan Nuwamban 2024 don mamaye yankin.

A cikin watanni tara tun daga lokacin, ta kai farmaki ta kasa tare da kai hare-hare ta sama sama da sau 500 a yankin Siyria.

Duk da cewa dan aiken musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan Syria ya yi Allah wadai da wadannan ayyuka, hukumomin Majalisar Dinkin Duniya ba su dauki kwararan matakai na mayar da martani ba.

Sakamakon haka, hare-haren Isra'ila, wanda ya yi daidai da halayenta a lokacin yakin basasa, na ci gaba ba tare da samun wata amsa daga kasashen duniya ba.

Maimakon kalubalantar ta'addancin Tel Aviv, kasashen duniya, musamman Amurka, sun mayar da hankali wajen tabbatarwa Netanyahu cewa zaman lafiyar Siyria ba zai yi barazana ga tsaron Isra'ila ba.

Dabarar a bayyane take karara: idan za a iya gyara Damascus ta hanyar shigar da Siyria ga Yarjejeniyar Abraham ta hanyar da ta dace da bukatun kasashen Gulf da Amurka, za ta daina zama kan gaba wajen kalubalantar Isra’ila, kuma a a zurfafa daidaita wa da juna.

Duk da haka, Isra’ila ta bambanta sosai daga wannan hangen nesa. Maimakon ganin sake hadewar Syria a matsayin garantin tsaro na dogon lokaci a gare ta, gwamnatin Netanyahu ta fi son jin dadin kai hare-hare da shiga tsakani.

A lissafin Tel Aviv, samar da Syria mai rauni, mai rarrabuwar kawuna zai tabbatar da mamaya da karfin ikon Isra'ila a yankin, maimakon sake gina ƙasar da ta iyaka da Turkiyya da Tekun Fasha.

Ana iya danganta zabin Isra'ila na ganin Syria mai rauni d ayadda take ta tsoma baki a harkokin kasar, da ma damuwarta cewa Syria mai zaman lafiya na iya kai wa ga samar da gwamnati mai adawa da gwamnatocin Isra’ila.

Ba kamar gwamnatin Assad ba, gwamnatin da ke samun goyon bayan mafi yawan al'ummar kasar, bayan samun kwanciyar hankali ta fuskar tattalin arziki da siyasa, za ta iya daukar mataki kan mamayar da Isra'ila ke kai wa tuddan Golan da ta mamaye.

Bugu da ƙari, a cikin 'yan kwanakin nan, Netanyahu ya ce, "Ni ba marar tunani ba ne, na san wanda nake hulɗa da shi" game da gwamnatin Syria.

A takaice dai, ga Washington, fifiko shi ne samar da Syria mai tsaro da zaman lafiya a yankin; ga Tel Aviv kuma, fifikon shi ne ci gaba da samun ikon kai hari kan yankin Syria yadda ta ga dama.

Yarjejeniyoyin Abraham, na bayyana yadda za a sulhunta wadannan tunani masu karo da juna da ba za su yiwu ba.

Turkiyya a matsayin mai daita wa da kawo salama

Watanni tara da suka gabata sun nuna cewa, yayin da Isra'ila ke tabarbarewa, Ankara na iya daidaita al’amura a Syria.

Haɗin gwiwar da Turkiyya za ta yi da Damascus na iya zama ingantacciyar hanyar samun kwanciyar hankali, tare da haɗin gwiwar soji don inganta horar da sojojin Syria, habaka kayan aiki da karfin iko.

Ga kasashen duniya kuma, darasin ya fito karara: aiki tare da kuma goya wa Turkiyya baya a rawar da za ta taka mai amfani, maimakon yin watsi da zaluncin Isra'ila, na iya zama hanya mafi tasiri wajen kawar da rikici a Syria.

Turkiyya, tare da tasirinta kan batun Syria da kuma diflomasiyyarta don kawo gyara a yankin, tana nuna ƙarfin iko a matsayin mai ɗaukar nauyi da hana ɓarna da faɗawa cikin rikicin da za a kasa shawo kansa.

Haɗin gwiwar Turkiyya da Qatar yana bayar da tsari may kyau. Kamar dai yadda na baya-bayan nan ke iya yiwuwa, kusantar juna tsakanin Turkiyya da Syria na iya rikide wa zuwa hanyar hadin gwiwa don dakile ta'addancin Isra'ila.

Duk wani hari ta sama na Isra'ila, na kara kusantar da Damascus zuwa ga Ankara, yayin da a lokaci guda ke kara kaifin fahimtar Turkiyya game da barazanar Isra'ila.

Yiwuwar hadin gwiwar soja, tattalin arziki, da siyasa tsakanin Turkiyya da Syria, musamman idan Washington ta rage goyon bayan da take bai wa 'yan ta'addar PKK/YPG, to hakan ne tsoron da Isra’ila ke ji game da kawancen.

A lokacin yakin basasa, Turkiyya ta yi nasarar kulla hulda da Rasha, Iran, da wadanda ba gwamnatoci ba; a sabon lokaci, duk da haka, yanzu ta sami Isra'ila a matsayin babbar abokiyar hamayyarta.

Kamar dai yadda Turkiyya ta hanyar shawarwarin Astana da Sochi ta samar da fagen gwagwarmaya da Rasha da Iran duk da cewa Amurka ta bar su su kadai, a wannan sabon mataki, za mu iya ganin wani tsari da Turkiyya ta koyi yadda za ta tinkara da kuma sarrafa fusatar Isra'ila.

Yayin da ayyukan sojan Turkiyya suka samar da sararin rayuwa ga 'yan adawar Syria tare da kawar da ta'addanci, yanzu muna fuskantar wani ma'auni inda dole ne Turkiyya ta goyi bayan zaman lafiya da daidaiton yankunan Syria tare da wanzuwar sojojinta kai tsaye.

Wannan dai yana da matukar muhimmanci ba wai kawai ta hanyar bayar da gudummawa ga zaman lafiyar kasar Syria ko kuma tabbatar da tsaron kasar Turkiyya a matsayin wani fanni na gasar samun karfin iko a yankin a tsakanin Turkiyya da Isra'ila ba, wanda hakan ke kara dora Turkiyya kan Isra'ila. Don haka, a wannan tsohon filin daga, wani sabon yaki na jiran Turkiyya.

Bayan shafe fiye da shekaru goma ana yakin basasa, Damascus da Ankara sun tsunduma cikin babban hadin kai.

Ga Syria, wacce karfinta ya ragu, wannan dabarar ita ce hanya daya tilo da ta dace don maido da kwanciyar hankali da daidaiton yankuna.

Wannan hadin kai na siyasa shi ne na samun isasshen lokaci: fita daga keɓantuwar diflomasiyya, kawo zuba jari da zai habaka tattalin arziki, sauƙaƙa hanyoyin dawowar Siriyawa daga ketare, da sake gina ikon ƙasar sannu a hankali.

Isra'ila kuma na ta yin aiki don kawar da wannan murmurewa da Syria ke yi. Syria mai zaman lafiya da kwanciyar hankali, musamman wadda ke samun goyon bayan wanzuwar Turkiyya, za ta iya kalubalantar hare-haren Isra’ila a kan iyakoki da sarrafa mayakan sa kai.

Yayin da Isra'ila ke neman tabarbarewa ta har abada, Turkiyya kuma na da damar assasa zaman lafiya mai dore wa, kuma wannan gwagwarmaya ce za ta fayyace shafin yankin na nan gaba.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us