TURKIYYA
2 minti karatu
Mummunan harin da aka kai caji ofis a yammacin Turkiyya ya yi sanadin shahadar 'yan sanda biyu
An kama wani matashi ɗan shekara 16 da ake zargi da kai harin bindiga a lardin Izmir na ƙasar Turkiyya, wanda kuma ya yi sanadin jikkata wasu 'yan sanda biyu.
Mummunan harin da aka kai caji ofis a yammacin Turkiyya ya yi sanadin shahadar 'yan sanda biyu
'Yan sanda sun yi gaggawar bazuwa a yankin, inda suka kafa matakan tsaro masu tsanani. / AA
8 Satumba 2025

'Yan sanda biyu sun yi shahada yayin da wasu biyun suka jikkata a wani harin bindiga da aka kai kan wani caji ofis a lardin Izmir da ke yammacin Turkiyya a ranar Litinin, inda aka kama wani matashi ɗan shekara 16, in ji jami'ai.

Matashin ya bude wuta da bindiga a caji ofis ɗin Salih İsgoren da ke yankin Balcova na Izmir.

Ministan Cikin Gida, Ali Yerlikaya ya bayyana wannan hari a matsayin "mugun abu," inda ya ce ya yi sanadiyyar shahadar 'yan sanda biyu, yayin da wani ya samu "mummunan rauni" kuma wani ya samu "rauni kaɗan."

"Wanda ake zargi a wannan al'amari, matashi ne mai shekara 16 mai suna E.B., an kama shi kuma an ƙaddamar da bincike," Yerlikaya ya rubuta a shafin X.

An kai jami'in da ya jikkata zuwa Asibitin Bincike da Aiwatarwa na Jami'ar Dokuz Eylul.

Ministan Shari'a, Yilmaz Tunc, ya sanar da cewa an fara binciken shari'a kan harin da Ofishin Babban Mai Shari'a na Izmir ke jagoranta.

"An fara binciken shari'a nan take daga Ofishin Babban Mai Shari'a na Izmir dangane da wannan al'amari, kuma an tura mataimakan babban mai shari'a biyu da masu shari'a shida," Tunc ya rubuta a shafin X, yana Allah wadai da harin bindigar.

Jami'an 'yan sanda sun bazama nan take a yankin, suna tsaurara matakan tsaro, kamar yadda rahotannin kafafen yada labarai suka bayyana.

Magajin garin Izmir, Cemil Tugay ya yi Allah wadai da wannan hari da ya kira na "mugunta," tare da aikewa da ta'aziyyarsa ga iyalan shahidan a wani rubutu a shafin X.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us