NIJERIYA
3 minti karatu
Mele Kyari: Babbar Kotun Tarayya a Nijeriya ta hana tsohon shugaban NNPC amfani da asusun bankinsa 4
Mai Shari’a Emeka Nwite ya ba da wannan umarnin ne ranar Talata bayan lauyar hukumar, Ogechi Ujam, ta nemi kotun ta hana amfani da asusun bankin guda huɗu.
Mele Kyari: Babbar Kotun Tarayya a Nijeriya ta hana tsohon shugaban NNPC amfani da asusun bankinsa 4
Mele Kyari shi ne tsohon shugaban kamfanin man Nijeriya / NNPCL
20 Agusta 2025

Babbar kotun Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ke Abuja ta ba da umarnin hana amfani na wucin-gadi da asusun banki huɗu da ke da alaƙa da tsohon shugaban kamfanin man Nijeriya, NNPCL, Mele Kyari bisa zarge-zargen almundahana.

Mai Shari’a Emeka Nwite ya ba da umarnin ne ranar Talata bayan lauyar hukumar EFCC, Ogechi Ujam, ta nemi kotun ta hana amfani da asusun guda huɗu na bankin Jaiz zuwa lokacin da hukumar za ta kammala bincike.

Alƙalin, a hukuncin da ya yanke, ya ce EFCC tana da hujja mai ƙwari, saboda haka ya amince da buƙatarta.

“Na saurari lauyar mai neman ɗaukar matakin kuma na duba hujjoji da bayanan da aka haɗa da buƙatar, na gane cewa buƙatar tana da ƙwaƙƙwarar hujja, kuma yanzu na ba da izinin aiwatar da ita,” in ji alƙalin.

Kana Mai Shari’a Nwite ya ɗage zaman kotun zuwa ranar 23 ga watan Satumba domin jin ba’asin wani rahoto game da batun.

Ranar 11 ga watan Agustan shekarar 2025 ne hukumar EFCC ta gabatar da buƙatar neman kotun ta hana amfani da asusun bankin na Kyari, “wanda ake gudanar da bincike a kansa a halin yanzu game da wani batu na laifukan haɗa baki da amfani da ofishinsa ta hanyar da bata dace ba da kuma halatta kuɗin haram zuwa lokacin da za a kammala bincike.”

A jikin wata takardar rantsuwa da ya haɗa da buƙatar, Amin Abdullahi, wani mai bincike  a  hukumar  EFCC, ya ce a ranar 24 ga watan Afrilu ne wata ƙungiya ta kai ƙarar Kyari hukumar kana hukumar ta yi bincike kan ƙarar.
Ya ce shi kansa yana cikin waɗanda aka bai wa aikin bincike game da ƙarar.

“Daga samun takardar ƙarar da muka nuna a sakin layi na huɗu, tawagata ta yi ayyukan bincike ciki har da neman bayanai daga bankuna,” in ji shi.

Ya ce bincike na farko ya nuna cewa biyu daga cikin asusun bankin na ɗauke da sunan Mele Kyari, yayin da saura biyu na ɗauke da sunan wata ƙungiya mai zaman kanta, Guwori Community Development Foundation Flood Relief.

Asusun da aka lissafa sun haɗa da da asusun Jaiz Bank mai lamba: 0017922724 da suna: Mele Kyari; da kuma asusun Jaiz Bank mai lamba: 0017922724 da suna: Mele Kyari;  da asusun Jaiz Bank mai lamba: 0018575055 da kuma asusun Jaiz Bank mai lamba: 0018575141 inda dukkansu biyu ke da suna “Guwori Community Development Foundation Flood Relief.”

Hukumar mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta kuma ce bincike na farko da ta gabatar kawo yanzu ya nuna cewa asusun bankin guda huɗu na da alaƙa da Mele Kyari, wanda ta yi zargin cewa yana amfani da su wajen karɓar kuɗaɗen haramun daga NNPC da wasu sauran kamfanonin mai da ke da alaƙa da NNPC.

“Bayanan banki sun nuna cewa waɗannan asusun Kyari ne yake juya akalarsu ta hannun ‘yan’uwansa da suke amfani da su a madadinsa,” in ji shi.

Abdullahi ya kuma ce binciken da aka gudanar kawo yanzu ya nuna “cewa naira N661,464,601.50, wanda ake zargin kuɗaɗen haramun ne, an adana su ne cikin asusun guda huɗu.

“Waɗannan kuɗaɗen an bi sahunsu zuwa Mele Kolo Kyari, wanda shi ne tsohon babban daraktan kamfanin mai na Nijeriya (NNPC).

“Ƙarin bincike ya nuna cewa kuɗaɗen da aka tura cikin asusun an sakaya su ne a matsayin kuɗin ƙaddamar da littafi da kuma ayyukan ƙungiya mai zaman kanta (NGO),” in ji shi.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us