Shugaba Bola Tinubu na Nijeriya ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ƙasar Brazil da nuna sufurin jirage kai-tsaye tsakanin ƙasashen Nijeriya da ƙasar da ta fi ƙarfin tattalin arziƙi a Kudancin nahiyar Amurka.
Ranar Litinin aka kammala yarjejeniyar a lokacin da Shugaban Tinubu ya kai ziyarar aiki Brasília, babban birnin ƙasar.
Wata sanarwar da maitaika wa Ministan Sufurin Jiragen Nijeriya kan harkar watsa labarai, Tunde Moshood, ya fitar ta ce an kammala yarjejeniyar ne a gaban Shugaba Bola Tinubu da Shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva da kuma Ministan Sufurin Jiragen Saman Nijeriya, Festus Keyamo.
Kazalika sanawar ta ce Festus Keyamo ne ya rattaba hannu a yarjejeniyar a madadin Nijeriya, yayin da Ministan Sufurin Brazil, Silvio Costa Filho, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar a madadin ƙasarsa.
Yarjejeniyar ta sufurin jiragen saman za ta samar da tsarin sufurin jirage kai-tsaye tsakanin Nijeriya da Brazil, da yiwuwar inganta kasuwanci da yawon buɗe ido da zuba jari da kuma hulɗar diflomasiyya.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, “[yarjejeniyar] ta kuma kasance wani muhimmin mataki cikin matakan inganta haɗin kai da ƙasashen duniya da kuma inganta sadarwar duniya.”
Tinubu ya tafi Brazil ne da wata tawagar da ta haɗa da ministan Kudi da tattalin arziƙi, Wale Edun da Ƙaramar Minister Harkokin Waje, Bianca Ojukwu da Ministan Noma, Abubakar Kyari da kuma manyan jami’an gwamnati.
Shugaban Brazilian ya yi maraba da yarjejeniyar, yana mai bayyana jajircewar gwamnatinsa ga faɗaɗa hulɗa da Nijeriya a fannonin sufurin jirage da noma da kuma ababen more rayuwa.
Ya bayyana yarjejeniyar sufurin jiragen saman a matsayar manuniyar dangantaka mai ƙarfin da ke tsakanin ƙasashen biyu da kuma damar zurfafa haɗin kai na tattalin arziƙi da al’ada.