Madogarar bincike kan abincin da aka sauya wa halitta (GMO), da dalilan karɓuwarsa a Nijeriya
KASUWANCI
6 minti karatu
Madogarar bincike kan abincin da aka sauya wa halitta (GMO), da dalilan karɓuwarsa a NijeriyaBatun GMO ya wuce zancen masu damuwa kan lafiya ko halascin cin irin wannan abinci, akwai siyasa, addini, da gogayyar tattalin arziƙin ƙasashen duniya cikinsa.
Akwai siyasa da addini, da gogayyar tattalin arziƙin ƙasashen duniya cikin batun GMO / Getty Images
8 awanni baya

A Nijeriya ana muhawara kan ci ko nomawa ko shigo da nau’in abincin da aka sauya wa halitta, wato GMO, yayin da hukumomin ƙasar suka fara neman malaman addini su shiga lamarin.

Gwamnati na ƙoƙarin gamsar da ‘yan ƙasar kan inganci da lafiyar iri da abincin da aka sauyawa halitta, don kawar da zargin masu cewa wasu cibiyoyin ƙasashen waje ne ke tursasa ƙasar.

A faɗin duniya, kayan abincin da aka sauya wa halitta, wato GMO wani batu ne da ake yawan maganganu da samun ruɗani da rarrabuwar kai kansa.

Batun GMO ya wuce zancen masu damuwa kan lafiya ko halascin cin irin wannan abinci, akwai siyasa, addini, da gogayyar tattalin arziƙin ƙasashen duniya cikinsa.

To mene ne GMO, ya ake samun sa, mene ne gaskiyar ingancinsa, kuma wa yake amfanarwa? 

Ma’anar GMO

Genetically Modified Organisms (GMOs), na nufin ƙananan halittun da aka yi wa kwaskwarima, ko dai a dabbobi ko ƙwayoyin halittar cikin iri ko ‘ya’yan itace.

Ana yawan alaƙanta batun sauya ƙananan halittu da harkar kayan abinci ne saboda kimiyyar sauya tsatson halittu, kimiyya ce da ake amfani da ita sosai a fannin binciken inganta iri.

Wani masanin kimiyyar sinadarai da ƙananan halittu, Dr Abdulrazak Ibrahim na Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria, ya bayyanawa TRT Afrika cewa hikimar sauya ƙananan halittu na nufin shigar da wata ɗabi’a a halitta.

Ɗabi’un sun haɗa da bijire wa ƙwari da cutuka, ko ƙarfafa juriyar shuka kan ƙarancin ruwa, ko ƙasa mai ƙarancin albarka, ko kuma haɓaka sinadaran gina jiki da ke cikin amfanin gona, don ya haura na asali.

Akan ƙarfafa tsatson iri ya iya kuɓuta daga ƙwarin cikin ƙasa, ko gubar sinadaran cikin ƙasa, ko don ya fitar da sinadarin kashe ƙwari, ko jure wa maganin kashe ciyawa, ko fitar da yabanya mai kyau, ko kyautata damar barbarar furanni, ko samun ƙarin ‘ya’ya, ko fitar da ‘ya’yan da wuri, ko samar da kara mai kauri da ƙwari, ko mai tsayi don ciyar da dabbobi.

Dr Ibrahim ya ce sauya halittar iri na da babban alfanu ga yankuna masu zafi, inda shuka kan fuskanci matsalar ƙwari da cutuka, fari da ɗaukewar ruwan damina.

Ke nan, sauya ɗabi’ar shuka don magance wannan matsalolin kan rage amfani da maganin ƙwari.

Yadda ake gane GMO

Idan ka kalli nau’in hatsi ko abincin da aka samar daga irin da aka sauya wa halitta, ba lallai ka gane shi da ido ba, saboda sauyin yana cikin sinadaran cikinsa ne masu girman ƙwayar zarra.

Kenan, hotunan da akan yaɗa na masara mai kalolin da ba a saba gani ba, ba hujja ce ta GMO ba.

Kala, fasali, ko girman hatsi na bambanta ne sakamakon dabarun auren shuka wanda fasaha ce ta daban.

Wato dai hatsin GMO a ido ba shi da bambanci da na gargajiya, kuma akan gane shi ne da tambarin da akan rubuta a jikin abincin, kamar yadda doka ta tanada.

Tarihin GMO a Nijeriya

A cewar Cibiyar Taron Tattalin Arziƙin Duniya, WEF, a 2015 an gudanar da killataccen gwajin noma irin GMO a karkarar Nigeriya.

Gwajin ya haifar da gagarumar nasara, kuma baya ga Nijeriya, ana gagarumin noman GMO don kasuwanci a Ghana, Burkina Faso, da Sudan, yayin da Afirka ta Kudu tun a 2000 ta fara noman GMO na masara, waken soya, da auduga.

A halin yanzu, a Nijeriya tuni an amince da nau’in wake na GMO mai jure ƙwari, da masara mai jure fari da kuma nau’in auduga.

Amfani da malaman addini a Nijeriya

A watan Yulin da ya gabata, Cibiyar Nijeriya kan Bunkasa Fasahar Halittu ta yi taron wayar da kan al’ummar Musulmi a Abuja, kan kayan gona da aka sauya wa halitta, don kawar da mummunar fahimta kan lamarin.

Darakta janar na cibiyar, Farfesa Abdullahi Mustapha ya ce abincin da aka sauya wa halitta ba shi da matsala ga mutane ko dabbobi ko muhalli, sannan yana jure fari, da haɓaka yalwar amfani, da rage yunwa, da azurta manoma.

Ya kuma tabbatar da cewa nau’in irin, kamfanonin Nijeriya ne ke samar da shi, kuma ya wajaba Nijeriya ta rungumi kimiyya da fasaha don tabbatar da wadatar abinci, da rage raɗaɗin sauyin yanayi.

Ya kuma ce sun gayyato shugabannin addini da na gargajiya kan batun, don su “sauya ra’ayoyin al’umma”.

Me ya sa ake hana GMO

Akwai wasu ƙasashe da suka haramta noma iri ko sayar da kayan abincin da aka sauya wa halitta, yayin da wasu ƙasashen suka amince da wasu bayan gudanar da bincike.

Dalilan kimiyya, da matsin lamba daga al’umma ko ƙungiyoyin addini, siyasa da masu zaman kansu, suna janyo haramta GMO.

Wasu manoma a Afirka suna tsoron harkar GMO saboda kallon sa a matsayin guba da za ta iya lahanta ƙasar nomansu ko gurɓata ingantaccen irin gargajiya, ko rusa farashin amfanin gona.

Wasu malaman addini suna sukar GMO don muradunsu na kiyaye tsarki, inganci da lafiyar abinci, da martaba halittar Allah yadda take a ɗabi’a babu sauyi.

Suna cewa sauya halittar iri tamkar nuna girman-kan ɗan’adam ne ga mahalicci, saboda juya zubin halitta zai iya barazana ga albarkatun duniya da cutar da lafiyar mutane.

A cewar hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ƙasashen da ke da takunkumi kan GMO a fannin abinci, yawanci suna yi ne saboda tantama kan ingancin lafiyarsa ga masu cin abincin.

Akwai gwaje-gwaje da aka yi kan dabbobi kamar birrai, ɓera da alade, amma an samu mabambantan sakamako.

Gaskiyar lamari shi ne, kowace ƙasa tana yanke hukunci kan nomawa ko shigo da kayan abincin GMO ne ba saboda kimiyya kacal ba. Akan yi ƙoƙarin kaucewa kace-nace da kare dabarun cinikayya, da ma siyasar duniya.

Kyautata amincewa da GMO

Masu so a rungumi GMO sukan yi nuni da tasirinsa wajen kawar da yunwa, musamman a wuraren da ke fama da fari ko yanayin damina mara tabbas, ko jinkirin faɗuwar damina da kuma ɗaukewarta da wuri, ko ƙarancin abinci da ambaliyar ruwa.

Sai dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce akwai hanyoyin magance yunwa a duniya ba sai ta amfani da GMO ba.

A ra’ayin Dr Abdulrazak Ibrahim, hanya mafi kyau don kyautata amincewa da GMO ita ce amfani da malaman gona, da samar da iri, da horar da manoma kan tasirinsa wajen karuwar arziƙinsu.

Sannan akwai batun tabbatar wa jama’a tsare-tsaren gwamnati kan kiyaye duk haɗarin da ka iya zuwa daga yawaitar amfani da GMO, da saka ido kan kimiyyar kwaskwarimar halitta.

A ƙarshe, kamar yadda Dr Ibrahim ya tabbatar wa TRT Afrika, kimiyyar GMO ta kawo nagartaccen sauyi a harkar kasuwancin hatsi kamar waken soya, auduga, da canola, tsakanin ƙasashen duniya ciki har da ƙasashe masu tasowa.

Sannan shakkun wasu manoma game da GMO ba ya rasa nasaba da tsada ko damar samun irin, da tsoron tasirinsa kan ƙasar noma.

Masanin ya ce yin aike tare da manoman a filayen gwada shuka da fayyace musu bambancinsa a riba, da bayyana matsala idan ta taso, shi ne zai taimaka wajen ƙarfafa imaninsu kan GMO.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us