NIJERIYA
2 minti karatu
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta kafa kwamitin bincike kan hatsarin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna
Kazalika Alkali ya ce kwamitin zai kuma ba shawara game da mafita na dindin da za ta hana sake aukuwar hatsarin.
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta kafa kwamitin bincike kan hatsarin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna
Kazalika Alkali ya ce kwamitin zai bayar da shawara game da mafita ta dindindin da za ta hana sake aukuwar hatsarin. / Nigerian Government
14 awanni baya

Ministan Sufurin Nijeriya, Said Alkali, ya kafa wani kwamitin bincike kan hatsarin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna da aka yi a garin Jere ranar Talata.

Wata sanarwa da daraktar watsa labarai ta ma’aikatar Sufurin, Misis Janet McDickson, ta fitar ranar Laraba a Abuja, ta ce kwamitin da ya ƙunshi masu ruwa da tsaki a lamarin zai binciki dalilan da suka janyo hatsarin.

Kazalika Alkali ya ce kwamitin zai bayar da shawara game da mafita ta dindindin da za ta hana sake aukuwar hatsarin.

Ministan ya ce kwamitin zai kuma ba da shawarwari game da yadda za a inganta sufurin jiragen ƙasa a Nijeriya.

Sanarwar ta ce ministan ya bayyana damuwa game da rashin aminci ga matafiya inda ya bayyana ‎daraktan da yake kula da ofishin babban sakataren ma’akatar sufuri Musa Ibrahim a matsayin shugaban kwamitin.

Mambobin kwamitin su ne: Farfesa Danwaka Shuaibu da Zirra Finbar da Mista Omotola Olusegun wanda zai kasance sakataren kwamitin.

‎Sauran mambonin sun haɗa da Dakta Kayode Opeifa (shugaban hukumar kula da layin dogo ta Nijeriya) da I.A Ebuniwe da wani wakilin kamfanin Technics Engineering Architecture Marketing Nig. Ltd da kuma wakilin kamfanin CCECC da kuma wani wakilin ƙungiyoyi masu zaman kansu.

Sanawar ta kuma ce za a samu namiji ɗaya da ta mace ɗaya waɗanda za su wakilci matafiya mata da maza a cikin kwamitin.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us