Hotunan yadda ake tashin talakawa masu kwana a titi a birnin Washington na Amurka
Hotunan yadda ake tashin talakawa masu kwana a titi a birnin Washington na Amurka
Matakin haɗin gwiwa na hukumomin tarayya wanda shugaban jam'iyyar Republican ya ba da umarnin yi don yakar laifuka a babban birnin ƙasar ya zama babban lamari sosai.
16 awanni baya

Daruruwan dakarun tsaron ƙasa na Amurka da aka fi sani da National Guard da motocin Humvee sun fara kare wasu wuraren tarihi a birnin Washington yayin da ƙungiyoyin agaji suka taimaka wajen kawar da tantunan mutanen da ba su da matsugunai a gabanin wani matakin tsaurara tsaro da ake tsammani, yayin da Shugaba Donald Trump ya ƙara karfin ikonsa kan 'yan sandan birnin.

Matakin haɗin gwiwa na hukumomin tarayya wanda shugaban jam'iyyar Republican ya ba da umarnin yi don yakar laifuka a babban birnin ƙasar ya zama babban lamari sosai, inda kafa wurin binciken da jami'ai suka yi a daren Laraba a daya daga cikin wuraren da mutanen da ba su da muhallai suka mayar tamkar kasuwar dare a birnin DC ya jawo zanga-zanga.

Fadar White House ta bayyana cewa an kama mutum 45 a daren Laraba, ciki har da mutum 29 da ke zaune a ƙasar ba bisa ka'ida ba, da suka haɗa da masu laifukan rarraba ko mallakar miyagun ƙwayoyi da ɗaukar makami a ɓoye da kuma kai hari kan wani jami'in tarayya.

An tura sojoji a wajen tashar Union Station yayin da aka fara aikin dakarun National Guard 800 da Trump ya ba da umarni, wanda ya haɗa da tsaron wuraren tarihi, sintirin tsaro na al'umma da kuma ayyukan kyautata muhalli, in ji Pentagon.

Ma’aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon ta ce ba za a ba sojojin makamai ba amma kuma ta ƙi bayar da karin bayani kan abin da ayyukan sintirin tsaro ko kyautata muhalli za su ƙunsa ko kuma yawan sojojin da aka riga aka tura kan tituna.

Manjo Micah Maxwell na rundunar tsaro ta National Guard ya ce sojojin za su taimaka wa jami'an tsaro a fannoni daban-daban, ciki har da wuraren kula da zirga-zirga da kuma hana taron jama'a tayar da hargitsi. Maxwell ya ce an horar da sojojin kan dabarun rage tashin hankali da kuma shawo kan mutane.

Fadar White House ta bayyana a ranar Alhamis cewa dakarun tsaron ba kama mutane suke yi ba, “kawai kare kadarorin gwamnati suke yi da samar da yanayi mai aminci ga jami'an tsaro don yin kame, da kuma rage laifukan tashin hankali ta hanyar kasancewa a wuraren jama'a da ake gani."

A lokaci guda, wasu marasa matsuguni a Washington sun tattara kayansu tare da taimakon masu sa kai daga wasu hukumomin birni. Ba a jefar musu da kayan ta ƙarfi ba, amma wata motar shara ta tsaya a kusa.

Wasu masu zanga-zanga sun riƙe alluna a kusa, wasu suna sukar gwamnatin Trump. Bayan marasa matsugunin sun tafi, wata motar gine-gine daga wata hukuma ta birni ta share ragowar tantunan.

Masu fafutuka sun yi tsammanin jami'an tsaro za su bazu a fadin DC daga baya a ranar Alhamis don rushe duk sauran sansanonin marasa matsuguni.

Tura sojojin a birnin Washington DC ya biyo bayan matakin Trump na tura dakarun tsaro don kwantar da tarzoma a birnin Los Angeles na California, wanda ya samo asali daga samamen da ake kai wa kan 'yan gudun hijira.

Wannan shi ne karo na farko tun shekarar 1965 da wani shugaban Amurka ya tura dakarun tsaro ba tare da amincewar gwamnan jiha ba.

Yawancin dakarun rundunar tsaro ta National Guard suna karkashin ikon gwamnoni na jihohi kuma dole ne sai an saka su a tsarin tarayya kafin su kasance cikin ikon Shugaban Ƙasa, amma a Washington waɗannan sojojin kai-tsaye suna ƙarƙashin Shugaban Ƙasa na Amurka ne kawai.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us