12 Agusta 2025
Rundunar Sojin Pakistan ta sanar a ranar Talata cewa ta kashe 'yan ta'adda 50 a kan iyaka da maƙwabciyarta Afghanistan a cikin kwanaki huɗu, a wani yanki mai cike da tashin hankali a kudu maso yammacin ƙasar da ke da wasu muhimman ayyukan more rayuwa na ƙasar China.
An kashe 'yan ta'addan ne a wani samame da aka ƙaddamar a ranar Alhamis, a cewar sanarwar da rundunar sojin ta fitar a Balochistan, inda 'yan ta'adda da 'yan a-ware ke gudanar da ayyukansu.
Za ku so karanta wadannan
Ba a iya tantance adadin waɗanda aka kashe ba a hukumance.