Wani rahoto na baya-bayan nan na Kungiyar Agaji ta Médecins Sans Frontières dangane da matsalar rashin abinci da yara suke fuskanta a arewacin Nijeriya ya ƙara fito da girman matsalar da ake ciki kuma masana sun fara tofa albarkacin bakinsu kan ya kamata hukumomi su tashi tsaye don kawo karshen wannan matsala.
Rahoton, wanda kungiyar agajin ta fitar a karshen watan jiya ta ce yankin arewacin Nijeriya yana fuskantar matsananciyar matsalar karancin abinci.
Kungiyar Médecins Sans Frontières (MSF) ta bayar da misali da Jihar Katsina inda jami’an kungiyar suke ganin ƙaruwar yaran da suke fama da matsalar rashin isasshen abinci kuma a wasu lokuta ma har ana samun asarar rayuka, kamar yadda rahoton ya bayyana.
Alkaluman da MSF ta tattara a karshen watan Yunin bana, sun nuna cewa akwai yara 70,000 a Jihar Katsina da suke fama da matsalar rashin isasshen abinci kuma jami’an kiwon lafiya na MSF sun ba su kulawa a cibiyoyin kungiyar, ciki har da yara 10,000 wadanda aka kwantar da su a asibiti saboda yadda matsalar ta ci jikinsu.
A cikin watanni shida wato tsakanin watan Janairu zuwa watan Yunin bana a Jihar Katsina, adadin yara da suka fada matsalar matsananciyar yunwa ya ƙaru da kaso 208 cikin 100, idan aka kwatanta da watanni shidan farko na shekarar 2024.
Sannan ka da a manta a jihar akwai wasu yaran har guda 652 da MSF ta ce sun mutu a cibiyoyinta saboda wannan matsala a cikin watanni shidan farko na wannan shekara.
Ko da yake ba wai kawai a Jihar Katsina ake fama da wannan matsala ba, matsala ce da ake fama da ita a sauran jihohin arewacin ƙasar kamar Sokoto da Zamfara da sauransu.
Ko da yake MSF, wacce ta fara aikace-aikacenta a Jihar Katsina a shekarar 2021, ta ce da hadin gwiwar hukumomin Jihar Katsina ta raba magunguna masu dauke da abinci da za su taimaka wajen magance matsalar yunwa (nutrition supplements) ga yara 66,000 a karamar hukumar Mashi, a wani yunkuri don ka da yaran su shiga mawuyacin hali.
MSF ta ce abin yana da tayar da hankali musamman idan aka yi la’akari da yadda kasar Amurka karkashin jagorancin Shugaba Donald Trump ta yanke tallafin kiwon lafiya da take bai wa kasashe masu tasowa ciki har da Nijeriya.
Kungiyar ta ce akwai buƙatar hukumomin arewacin ƙasar su tashi tsaye don magance wannan matsala.
Mutuwar yara 40 a ɗan ƙaramin lokaci
Wani likita wanda yake aiki a Jihar Katsina tare da Kungiyar MSF kuma ya bukaci mu sakaya sunansa, ya ce matsalar ta wuce duk yadda ake tunani.
Likitan ya ce matsala ce babba don akwai ranakun da ake kwantar da yara 100 zuwa 150, ban da wadanda suke rasa rayukansu.
Ya ce akwai ranar da yara kimanin 40 da suka mutu a asibiti daya cikin asibitoci biyu da MSF take da su a jihar.
Likitan ya ce yara 652 da rahoton ya ce sun mutu a cikin wata shida, adadi ne da bai hada da yaran da suka mutu a gida ba, wato wadanda ba a kai ga kai su asibiti ba. Likitan ya ce idan aka hada da su, to adadin da rahoton ya bayyana ya zarta 652.
Likitan ya kuma ce hatta yaran da suka tsira da matsalar akwai ƙalubalen da za su iya fama da shi zuwa gaba. Bincike ya nuna cewa matsalar rashin isasshen abinci da yara suke fama da ita za ta iya rage musu kaifin ƙwaƙwalwarsu idan sun girma, musamman ta fuskar ƙoƙarinsu a makaranta da kaifin basirarsu.
Masu sharhi na ganin sai an sake tashi tsaye haiƙan wajen magance wannan bala’i da ke shafar yara, waɗanda su ne manyan gobe. Kuma hakan na buƙatar haɗa hannu da ƙarfe tun daga kan gwamnatoci da ƙungiyoyi masu zaman kansu da ma al’umma gaba ɗaya.