Yadda bikin Rahama Sadau ya zo da mamaki amma ya samu yabo
Yadda bikin Rahama Sadau ya zo da mamaki amma ya samu yabo
An yi bikin fitacciyar tauraruwar finafinan Hausa Rahama Sadau, wanda ba a kururuta ba, duk da a baya ta taɓa cewa bikinta ba zai ɓuya ba.
15 Agusta 2025

“Rahama Sadau za ta yi aure ba da jimawa ba.” Wannan ce amsar da fitacciyar tauraruwar finafinan Hausa Rahama Sadau ta bai wa TRT Afrika Hausa, shekaru biyu da suka gabata.

Yayin tattaunawar ta musamman a Istanbul, an tambayi Sadau ko wane ne angon nata, sai ta ka da baki ta ce “Angon Rahama Sadau ai ba zai ɓuya ba”.

Lokaci alƙali, yanzu dai a watan nan na Agustan 2025, Rahama Sadau ta amarce, sai dai bikin nata ya zo da mamaki, saboda ba a kururuta shi ba. Hasali ma sai ranar ɗaurin auren zancen ya baza gari.

Wani ƙarin abin mamaki shi ne yadda har yau ake ta muhawara kan wane ne angwan nata, kasancewar har yau ba a yi hidimomin bikin ba, balle a ga ango da amarya suna takawa a wajen dina.

Ɗaurin auren ya gudana ne a masallacin Unguwar Rimi da ke garin Kaduna a Nijeriya, kuma rahotanni sun ce an biya sadakin naira 300,000 kamar yadda shaidu suka tabbatar.

An bayyana sunan angwan da Ibrahim Garba, kuma ‘yan-uwa da makusanta, da abokan arziƙin Sadau sun halarcin ɗaurin auren.

Rahama Sadau da kanta ta tabbatar da labarin auren a shafinta na soshiyal midiya, inda ta ce: “Bismillahir Rahmanir Raheem… Alhamdulillah, an ɗaura aurena yau. A hukumance sunana matar aure. Na shiga sabuwar rayuwa kuma zuciyata na cike da godiya da murna.”

Wace ce Rahama Sadau?

Rahama Sadau shahararriyar ‘yar fim ce kuma mai shirya fina-finai. Jaruma ce da ta yi suna a masana’antar Kannywood ta fina-finan Hausa, da ma Nollywood ta finafinan Nijeriya da ake yi da Ingilishi.

An haifi Rahama Sadau a 1993 a Kaduna, kuma ta shiga harkokin finafinai ne a shekarar 2013 a fim ɗin Hausa na “Gani ga Wane”, tare da jarumi Ali Nuhu.

Daga nan an fara ganin ta a shirye-shiryen Turanci irinsu Sons of the Caliphate, Up North, Zero Hour, da Chief Daddy 2. Hazaƙarta da ƙazonta sun sa ta lashe kyaututtuka da dama saboda ƙoƙarinta.

Auren Sadau ya ɗauki hankulan jama’ar Nijeriya bakiɗaya, musamman a arewa, inda aka yi ta tattauna batun a shafukan sada-zumunta.

Masoya da abokan aikin Sadau sun yi ta miƙa saƙonnin taya murna ga tauraruwar, ciki har da sanannun taurarin finafinan Hausa, mata da maza.

Batun rashin bayyana bikin Sadau da kuma fito da hotunan angwan nata bai hana mutane yin sharhi kan bikin ba. An yi tattauna yadda auren ya zo da mamaki kasancewa ba a zaci Sadau za ta zaɓi yin biki a asirce ba.

Yabo da jinjina

Baya ga mamaki, wasu masu sharhi sun yaba wa Sadau kan zaɓar yin ƙaramin shagali tare da ‘yan uwa, maimakon cika gari da gagarumin biki na nuna isa ko fifiko ga jama’a gamagari.

Daga Kaduna zuwa, Kano, Sokoto zuwa Lagos, masoya Sadau sun yi ta mata addu’ar samun rayuwar aure tagari, har wasu suka ba da shawara ga ‘yan-baya cewa su kwaikwayi salon Sadau.

Masu sharhi na ganin yin ƙaramin biki irin na Rahama Sadau yakan rufe bakin ‘yan gulma, da masu suka, tare da ƙarawa ma’auratan girma a idon manya, da ba su damar fuskanta rayuwarsu cikin aminci ba tare da hayaniya ba.

A yanzu dai za a jira ganin ko tauraruwar za ta ci gaba da shiga finafinai, sannan ko za a ringa ganin ta a bukukuwan taurarin arewa da na Nijeriya, tare da angon nata da ake son gani ruwa a jallo.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us