Fiye da mutane 40 ne suka ɓace bayan wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji aƙalla 50 ya kife a Jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Nijeriya, kamar yadda Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta bayyana.
"An ceto kusan mutane 10, yayin da fiye da fasinjoji 40 suka ɓace," a cewar wata sanarwar da NEMA ta fitar a ranar Lahadi.
Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su na kan hanyarsu ta zuwa kasuwar Goronyo ta mako-mako, yayin da kwale-kwalen ɗauke da fasinjoji da kayayyaki ya kife.
Darakta Janar na Hukumar NEMA, Zubaida Umar, ta ce cikin gaggawa hukumar ta ƙaddamar da bincike bayan samun rahoton faruwar lamarin.
Ƙoƙarin ceto
Ofishin hukumar NEMA da ke jihar Sokoto tare da haɗin gwiwar hukumomin yankin da kuma jami’an bayar da agajin gaggawa, sun tsananta bincike don ceto fasinjojin da suka ɓata.
"Hukumar NEMA na ƙara tabbatar wa jama'a kuɗirinta na ceton rayuka, da samar da sabbin bayanai kan lokaci da kuma samar da duk wani tallafin da ya dace ga iyalan wadanda abin ya shafa," in ji Sanarwar.
A yawan samun haɗura masu alaƙa da kifewar kwale-kwale akai-akai a Nijeriya, yayin da hanya sufurin ruwa ya kasance wanda ake amfani a matsayin hanyar zirga-zirga ta yau da kullun, musamman a yankunan karkara masu ruwa.
A watan Nuwamban bara mutane da dama ne suka mutu a lokacin da wani kwale-kwalen da ke ɗauke da fasinjoji kusan 200 ya kife a mashigin Dambo-Ebuchi na kogin Niger da ke yankin arewa ta tsakiyar jihar Neja.
Mahukunta a Nijeriya dai na yawan ɗora alhakin kifewar kwale-kwalen kan lodi fiye da ƙima da rashin kulawa da rashin kyawun yanayi da kuma rashin ɗaukar matakan kariya.