AFIRKA
2 minti karatu
Fiye da mutum 22 sun rasu sakamakon ruftawar wuraren haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba a Ghana
Hukumar Kawar da Afkuwar Bala’i ta Ghana ta ce haramtattun ramukan haƙar ma’adinai waɗanda aka yi watsi da su a Yankin Tsakiyar ƙasar ne suka yi sanadin mutuwar mutanen a cikin watanni bakwai da suka gabata.
Fiye da mutum 22 sun rasu sakamakon ruftawar wuraren haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba a Ghana
Mutanen sun mutu ne a cikin watanni bakwai da suka gabata / Reuters
7 awanni baya

Fiye da mutum 22 sun rasu bayan sun rufta a cikin haramtattun ramukan haƙar ma’adinai da aka yi watsi da su a Yankin Tsakiyar Ghana a cikin watanni bakwai da suka gabata, a cewar Kwesi Dawood, Daraktan Yanki na Hukumar Kawar da Afkuwar Bala’i ta Ƙasa (NADMO).

Ya bayyana cewa waɗannan ramuka da aka yi watsi da su sun halaka masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba waɗanda ake kira ‘yan galamsey haka kuma ramukan sun yi ajalin waɗanda ba ruwansu ma da haƙar ma’adinai – musamman mata da yara.

Mista Dawood ya bayyana wannan matsala a matsayin abin da yake “matukar tayar da hankali” inda ya yi gargaɗin cewa yawan mutanen da lamarin ya shafa na iya zarta hakan sakamakon rashin samun rahotannin afkuwar irin waɗannan lamura.

Ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai bayan taron Majalisar Tsaron Yanki, inda aka ƙaddamar da kwamiti naa musamman domin ƙwato wuraren hakar ma’adinai haramtattu a dukkan ƙananan hukumomin da ake haƙar ma’adinai na yankin.

Wannan kwamiti zai yi aiki a Assin North, Assin Central, Upper Denkyira East da West, Twifo Ati-Morkwa, Twifo Hemang Lower Denkyira, da kuma Karamar Hukumar Komenda-Edina-Eguafo-Abrem, kuma ya ƙunshi jami’an tsaro, NADMO, ‘yan majalisa, Hukumar Kula da Muhalli, Hukumar Ma’adinai, da kafafen yaɗa labarai.

Mista Dawood ya ce wannan shiri na nufin magance lalacewar muhalli da matsalolin da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ke haifarwa.

 Haka kuma, wannan na cikin wani ɓangare na shirin gwamnati na mayar da wuraren da aka lalata ta hanyar galamsey zama filayen noma da kuma gonakin shuka bishiyoyi – wani aiki da Ministan Yanki, Ekow Payin Okyere Eduamoah, ke jagoranta.

A wani ɓangare na wannan yunƙuri, an riga an tura manyan injina, sannan za a raba iri na amfanin gona kyauta ga al’ummomi domin ƙarfafa shuka a wuraren da aka gyara, wanda zai samar da hanyoyin dogaro da kai.

Mr. Dawood ya yi kira ga masu haƙar ma’adinai ba tare da izini ba su daina ayyukansu na cutarwa, su kuma shiga cikin wannan yunƙuri dawo da martabar gonaki da samar da abinci a ƙasar.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us