Dakarun Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa Maso Gabas ta Operation Hadin Kai sun kashe wasu mutum 12 da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram/ISWAP ne a wasu jerin samame da suka kai a wurare daban-daban na Ƙaramar Hukumar Mafa a Jihar Borno.
Ƙaramar Hukumar Mafa na da nisan kusan kilomita 59.8 daga Maiduguri, babban birnin jihar.
Sojojin sun samu nasara ne bayan sun samu bayanan sirri da kuma bayanai daga na’urorin leƙen asiri na Rundunar Sojin Sama, waɗanda suka samar da bayanai kai tsaye domin aiwatar da luguden wuta kan ‘yan ta’addan.
Wannan haɗin gwiwar ya kai ga kwato sansanonin ’yan ta’adda a yankunan.
Dakarun sun ƙwato bindigogin AK-47 guda takwas da jigidar harsasai guda takwas cike da harsasai nau’in 7.62mm, tare da tarin miyagun ƙwayoyi da kayan jinya da ’yan ta’addan ke amfani da su.
Hukumomin soji sun yaba wa dakarun bisa ƙoƙarinsu da jajircewa, tare da ƙarfafa musu gwiwa kan su ci gaba da kai farmaki.
Tun bayan fara rikicin Boko Haram a shekarar 2009, an kashe dubban mutane, yayin da fiye da mutum miliyan biyu aka raba da muhallansu a jihohin Borno, Yobe da Adamawa, a cewar rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya.