NIJERIYA
2 minti karatu
EFCC ta yi ƙarin haske kan samamen da ta kai Obasanjo Presidential Library
A sanarwar da ta wallafa a shafinta na X, hukumar EFCC ta ce ta ƙwace motoci 18 da wayoyi a hannun mutanen da ake zargi da damfarar.
EFCC ta yi ƙarin haske kan samamen da ta kai Obasanjo Presidential Library
Olusegun Obasanjo / REUTERS
11 Agusta 2025

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati, EFCC, ta yi ƙarin haske kan samamen da ta kai  Obasanjo Presidential Library (OOPL) da ke birnin Abeokuta a Jihar Ogun da ke kudancin ƙasar.

Jaridun Nijeriya dai sun ambato hukumar gudanarwa ta OOPL tana ƙorafi game da abin da ta kira samamen tashin hankali da jami’ai fiye da 50 ɗauke da bindigogi suka kai Ɗakin Karatun da misalin ƙarfe biyu na dare.

Jaridun sun ambato sanarwar hukumar gudanarwar tana cewa jami’an EFCC sun kutsa ɗakin karatun suna “harbi, da barazanar kashe mutane tare da sanya fargaba ga baƙi da mazauna wurin.”

Hukumar gudanarwar OOPL ta ce jami’an EFCC sun yi dirar mikiya kan wasu mutane da ke biki a cikin otal ɗin da ke ginin ɗakin karatun cikin dare ba tare da gabatar da takardar sammaci ba.

Duk da cewa ba ta ambaci sunan ɗakin karatun na OOPL ba, hukumar EFCC ta tabbtar da cewa ta kai samamen a wani otel a birnin Abeokuta inda ta kama waɗanda ake zargi da damfarar intanet da aka fi sani da ‘yan Yahoo guda 93.

 A sanarwar da ta fitar a shafinta na X, hukumar EFCC ta ce ta ƙwace motoci 18 da wayoyi daga hannun mutanen da ake zargi da damfarar.

Sai dai kuma hukumar gudanarwa ta OOPL ta ce duk da cewa jami’an EFCC sun yi iƙirarin cewa sun yi aikin ne bisa bayanan sirrin da suka samu, ‘yan sandan da ke aiki a bakin ƙofar ɗakin karatun da ma waɗanda aka gayyato daga waje domin bikin sun ce ba su san da zuwa jami’an EFCC ɗin ba.

Kazalika sanarwar hukumar gudanarwar OOPL  ta ce wasu mutane sun ji rauni yayin da suke ƙoƙarin tsere wa jami’an EFCC.

Ta kuma ce tana bincike game da samamen EFCC ɗin, tana mai cewa za ta kai maganar gaba.

Ɗakin Karatu na Shugaba Olusegun Obasanjo dai ɗakin karatu ne da ke da otal da wuraren shaƙatawa da ma wuraren taro a kan wani fili da ya kai kadada 32.

Kazalika a lokacin Shugaban Obasanjo ne aka kafa hukumar EFCC.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us