Ƙungiyar Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) mai alaƙa da Al Qaeda wadda ke iƙirarin jihadi ta ɗauki alhakin kai wasu hare-hare a sansanonin soji biyu na Jamhuriyar Benin da ke arewacin iyakar ƙasar a ranar Alhamis.
Majiyoyin tsaro sun bayyana aƙalla sojoji 70 aka kashe a yayin harin da aka kai, wanda shi ne hari mafi muni a kan sojojin Benin da aka taɓa kaiwa.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ta kafar da take yaɗa farfaganda, JNIM ta yi iƙirarin kai hari kan wasu sansanonin soji biyu da ke kusa da kan iyaka da Burkina Faso da Nijar, yankunan da suka yi fice wajen faɗaɗar kungiyoyin 'yan ta'adda masu ɗauke da makamai a yankin Sahel.
Kungiyar ta kuma fitar da hotuna da ke nuna ganimar yaƙi mai yawa da suka samu waɗanda suka haɗa da bindigogin M2HB na Amurka, da roka PP87 samfurin ƙasar Sin, jirage marasa matuka, na’urorin harba roka da jigida ta harsashi fiye da 300. Irin waɗannan kayayyakin da ƙungiysr ta yi baje-kolinsu ya nuna irin yadda ƙungiyar ta samu kayan aiki a harin da ta kai.
Zuwa yanzu dai gwamnatin Benin ba ta mayar da martani a hukumance game da wannan lamarin ba.
Sai dai wasu majiyoyi na tsaro sun tabbatar da cewa an samu mutuwar sojoji da dama kuma an tura ƙarin sojoji zuwa yankin domin samar da tsaro.