Rundunar Sojin Saman Nijeriya (NAF) ta kashe 'yan ta'addar Boko Haram sama da 15 a yankin Zuwa da ke dajin Sambisa a arewa maso gabashin Nijeriya, kamar yadda wani jami'i ya bayyana a ranar Alhamis.
Rundunar ta kashe 'yan ta'addar Boko Haram sama da 15 a ranar Larabar da ta gabata a wani bangare na Farmakan Hadin Kai na Hadin Gwiwa da rundunar hadin gwiwa ke kai wa a yankin Arewa maso Gabas, a cewar sanarwar da kakakin rundunar sojin sama, Ehimen Ejodame ya fitar.
Ya kara da cewa harin da aka kai ta sama ya nuna ingancin samun inda aka nufa, ƙarfin isa da kuma azama wajen yaƙi da ta’addanci.
"A ranar 3 ga Satumban 2025, wani shiri na tsanaki da aka aiwatar ya nufi wata sabuwar maboyar 'yan ta'adda da aka gano a yammacin Zuwa da ke Dajin Sambisa."
‘An rushe muhimman matsugunai da yawa’
"Bayan samun ingantattun bayanan sirri da sanya idanu da aka tabbatar, hare-haren sun nufi maboyar mayaka da kwamandojin da ke da alhakin tashe-tashen hankula a kwayen Bitta."
“Hare-Haren sun yi muni, inda aka kashe ‘yan ta’addar Boko Haram sama da 15 tare da ruguza wasu muhimman gine-gine masu muhimmanci ga ayyukansu,” in ji sanarwar.
Wannan nasara ta baya bayan nan ta nuna jajircewar da rundunar sojin sama ke yi na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya tare da tallafa wa sojojin kasa a ayyukan hadin gwiwa na tarwatsa cibiyoyin ‘yan ta’adda.
Sanarwar ta kara da cewa, "Rundunar Sojin Saman Nijeriya na ci gaba da tsaya wa a matsayin jigon sanya idanu, kwarewa, da kuma jajirce wa wajen tabbatar da tsaron kasa."
Boko Haram kungiya ce ta 'yan ta'adda da ke da hedkwata a Arewa maso-gabashin Najeriya, tana kuma kai hare-hare a kasashen Chadi, Nijar da Kamaru.
Kungiyar ta yi kaurin suna wajen kai munanan hare-hare kan fararen hula da jami’an tsaro da cibiyoyin ilimi, ciki har da harbe-harbe da tayar da bama-bamai da kuma garkuwa da mutane.