Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da ayyukanta na sama masu muhimmanci a arewa maso-gabashin Nijeriya saboda tsananin karancin kudade.
Hukumar Ayyukan Jinƙai ta Sama ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHAS) da Shirin Samar da Abinci na Duniya ke jagoranta, ta kawo karshen ayyukanta a kasar a makon da ya gabata bayan kusan shekaru 10 suna jigilar kayan tallafi da ma’aikata ta sama.
“A 2024, UNHAS sun yi jigilar sama da fasinjoji 9,000. A wannan shekarar, ma’aikatan jinƙai 4,500 sun dogara kan kan ayyukansu don zuwa yankunan da rikici ya shafa,” in ji Stephane Dujarric, kakakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya yayin tattaunawa da manema labarai a birnin New York na Amurka.
Ya ci gaba da cewa UNHA ba za su iya ci gaba da ayyuka ba tare da kudade ba.
Ya ce tsawon shekaru tara, ayyukan sun yi jigilar ma’aikatan jin kai, kayan magunguna. da kayayyaki masu muhimmanci zuwa yankunan da ke fama da rikici a jihohin Yobe da Borno, da ke kasar da take fuskantar rikici tsawon shekaru 16, kuma ba ta ingantattun hanyoyin mota.
Dakatar da ayyukan na zuwa ne a yayin da Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya ke fuskantar tsananin rashin kudade.
A watan Yulin bana, shirin ya yi gargadin cewa dole na iya tirsaa su dakatar da ayyukan gaggawa na bayar da abinci ga mutane miliyn 1.3 a arewa maso-gabashin Nijeriya.
Darakta Mai Kula da Shiyyar Yammacin Afirka a Shirin Samar da Abinci na MDD, Margot van der Velden ta fada wa ‘yan jaridu a New York cewa ana bukatar makudan kudade don ci gaba da ayyuka a Nijeriya.
“Ana bukatar dala miliyan 5.4 don ci gaba da ayyuka a watanni shida masu zuwa. Ba tare da wadannan kudade ba, ayyukan jinƙai a arewa maso-gabashin Nijeriya na fuskantar hatsarin dakatarwa daga mutanen da ya kamata su samu tallafin.” in ji van der Velden.
Majalisar Dinkin Duniyar dai ta yi gargadin cewa sakamakon da zai biyo bayan dakatar da ayyukan na UNHAS zai iya zama mummuna.