TURKIYYA
2 minti karatu
Turkiyya ba za ta taɓa yin shiru game da zaluncin Netanyahu kan Falasɗinawa ba: Erdogan
"Duk da rashin adalci da zalunci da ake yi a yankinmu, ba za mu taɓa yanke ƙauna ba," a cewar shugaban Turkiyya.
Turkiyya ba za ta taɓa yin shiru game da zaluncin Netanyahu kan Falasɗinawa ba: Erdogan
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan / AA
4 Satumba 2025

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jaddada cewa ƙasarsa ba za ta taɓa zuba ido tana kallo ana cutar da Falasɗinawa da hare-haren Isra'ila ba, inda ya caccaki Firaminista Benjamin Netanyahu.

"Ba za mu ci gaba da yin shiru tare da zuba ido game da irin wahalhalun da Netanyahu ya yake jefa Falasɗiawa a ciki ba," in ji Erdogan a ranar Laraba, yayin da yake jawabi a makon buɗe taron Maudili a Ankara.

Shugaban ya ƙara da cewa damuwar Turkiyya ta wuce iyakokinta, yana mai jaddada haɗin kai domin ceto ƙasashen Musulmai da ke fama da tashe-tashen hankula.

"Rabin zuciyarmu yana nan; sauran rabin kuma yana Gaza da Falasɗinu da Yemen da Sudan da kuma Afghanistan, inda al’ummar Musulmai suke jin raɗaɗin rauni da kuma jinin da ake zubarwa,’’ in ji shi shugaban.

Da yake jaddada muhimmacin haɗin kai, Erdogan ya bayyana cewa: "Muna ɗaukar dukkan Musulmai a matsayin tubalin gini iri ɗaya, wato sassan jiki ɗaya."

Duk da tashe-tashen hankula a yankin, shugaban ya buƙaci jajircewa da kuma tsayin-daka kan gaskiya.

"Ba mu yanke ƙauna ba, kuma ba za mu taɓa yanke ƙauna ba. Duk da rashin adalci da kuma zalunci a yankinmu, ba za mu taɓa yin ƙasa a gwiwa ba," in ji shi.

Isra'ila ta ƙaddamar da ƙazamin farmaki na soji a Gaza, inda ta kashe Falasɗinawa fiye da 63,700 tun daga ƙarshen shekarar 2023.

Hare-haren da sojojin suka kai sun lalata yankin wanda ke cikin yanayin tsananin yunwa da Isra'ila ta haddasa.

A ranar 8 ga watan Agusta, majalisar ministocin tsaron Isra'ila ta amince da wani shiri na Firaministan ƙasar Benjamin Netanyahu kan sake mamaye Gaza, wanda zai fara da Birnin Gaza a hankali.

A watan Nuwamban da ya gabata ne kotun hukunta manyan laifuka ta ƙasa da ƙasa ta bayar da sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaronsa Yoav Gallant bisa laifukan yaki da cin zarafin bil'adama a Gaza.

Har ila yau Isra'ila na fuskantar shari'ar kisan kiyashi a kotun ƙasa da ƙasa kan yaƙin da take yi a yankin.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us