Ranar Alhamis 27 ga Maris Barcelona ta karɓi baƙuncin Osasuna a wani kwantan wasa a Gasar LaLiga, inda to doke baƙin nata da ci 3-0.
Nasarar ta sa Barca ta ba da tazarar maki 3 a saman teburin LaLiga da jimillar maki 63, sama da mai biye mata Real Madrid, bayan buga wasanni 28.
Sai dai wasan ya bar baya da ƙura, saboda Osasuna na zargin Barcelona ta karya wata dokar FIFA kan amfani da wani ɗan wasa yayin karawar.
Osasuna na zargin cewa ɗan wasan baya na Barcelona, Inigo Martinez wanda ɗan asalin Sifaniya ne, bai cancanci buga wasan ba.
A kakar bana tauraruwar Martinez na haskakawa tun bayan zuwan sabon koci Hansi Flick ƙungiyar, wanda ya sa ɗan wasan ya samu kiranye daga tawagar ƙasarsa Sifaniya a watan nan.
Dokar FIFA
Sai dai ɗan wasan ya samu rauni a gwiwa wanda ya tilasta masa baro tawagar Sifaniya, inda aka maye gurbinsa da ɗan wasan Bournemouth, Dean Huijsen.
Bayan ya baro tawagar ta Sifaniya, Martinez ya dawo ƙungiyarsa ta Barcelona inda ya buga wasan da suka yi nasara kan Osasuna ranar Alhamis.
A yanzu dai, shafin Goal ya ambato wata jaridar wasanni ta Sifaniya, Diario Sport, na cewa Osasuna na duba yiwuwar shigar da ƙorafi kan Barcelona saboda zargin taka dokar FIFA dangane da saka ɗan wasan da ya baro tawagar ƙasarsa.
Osasuna na ganin cewa, bai kamata a ce Martinez ya buga wasan ba saboda dokar FIFA ta ce ‘yan wasan da suka baro tawagar ƙasarsu ba za su buga wa ƙungiyarsu ba sai bayan aƙalla kwanaki biyar, face idan hukumar ƙwallo ta amince masa ya buga.