WASANNI
2 minti karatu
UEFA ta ci tarar Yamal da Lewandowski kan shan ƙwayoyin kuzari, ta hukunta kocin Barcelona
Hukumar ƙwallo ta Turai, UEFA ta hukunta 'yan wasan Barcelona Lamine Yamal da Robert Lewandowski, da kuma dakatar da kocin Barca wasa guda.
UEFA ta ci tarar Yamal da Lewandowski kan shan ƙwayoyin kuzari, ta hukunta kocin Barcelona
/ AFP
8 Agusta 2025

Rahotanni daga hukumar ƙwallo ta Turai, UEFA na cewa ta ci tarar 'yan wasan Barcelona biyu, Lamine Yamal da Robert Lewandowski, tarar euro 5,000 kowannensu.

Wannan hukuncin na zuwa ne bisa laifin ‘yan wasan na rashin bin tsarin dokar hana shan ƙwayoyin ƙara kuzari a wasan da Barcelona ta buga na ƙarshe a gasar Zakarun Turai.

Laifukan sun auku ne a wasan Barcelona da Inter Milan a zagaye na biyu na wasan dab da na ƙarshe na gasar da aka buga a Italiya.

An tashi wasan ne da rashin nasara a ɓangaren Barca, inda ta sha kaye da ci 4-3 bayan ƙarin lokaci, wanda ya janyo aka fitar da su daga gasar da PSG ta ɗaga kofin a ƙarshe.

Dakatar da Flick

Rahotannin sun ce UEFA ta hukunta cewa ‘yan wasan biyu saboda ba su yi biyayya ga jami’in hana ta’ammuli da ƙwayoyin kuzari na hukumar ba.

Bugu da ƙari, ba su kai kansu kai-tsaye zuwa ofishin gwajin shan ƙwaya ba, kamar yadda doka ta tanada, wanda shi ya janyo musu wannan ƙaramar tara.

Shi ma kocin Barcelona, Hansi Flick bai tsira ba, saboda hukumar UEFA ta ci tarar sa euro dubu 20,000, sannan ta dakatar da shi tsawon wasa guda.

An samu Flick wanda ɗan asalin Jamus ne da laifin saɓa babbar dokar ɗa’a da saɓa ƙananan dokokin ɗa’a.

Haka ma mataimakin Flick, Marcus Sorg wanda ya samu tara. Duka hukuncin za su yi aiki nan take kuma za su yi tasiri kan wasannin Barcelona na gasar Turai mai zuwa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us