Hukumar ba da tallafin abinci ta duniya (WFP) ta yi gargadin cewa tallafin abinci ga miliyoyin ‘yan gudun hijiran Sudan a cikin unguwanni huɗu za su iya rasa abinci cikin watanni biyu masu zuwa idan ba a sami ƙarin kuɗi ba.
Sama da ‘yan gudun hijira miliyan huɗu da suka tsere daga yaƙin basasan da ake yi suna cikin barazana, in ji Shaun Hughes, shugaban ɓangaren ba da agajin gaggawa na hukumar WFP a rikicin yankin Sudan.
"Idan ba a sami ƙarin kuɗi ba, dukkan ‘yan gudun hijira za su fuskanci ragin tallafi cikin watannin da ke zuwa," kamar yadda Shaun Hughes, shugaban ɓangaren ba da agajin gaggawa na hukumar WFP a rikicin yankin Sudan, ya shaida wa wani taron manema labarai a Geneva, yana mai buƙatar a ba da dala miliyan 200 cikin watanni shida.
"Game da ƙasashe huɗu — Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da Masar da Ethiopia da kuma Libya — ayyukan hukumar WFP sun rasa kuɗi sosai ta yadda dukkan tallafi ka iya ɗaukewa cikin watannin da ke zuwa yayin da kuɗaɗen ke ƙarewa," a cewarsa, inda ya bayyana daga baya cewa wannan ka iya faruwa cikin watanni biyu.
Yunwa mai tsanani
A halin yanzu, mutum miliyan 24.6 million, kimanin rabin adadin mutanen Sudan, suna fama da tsananin rashin tabbacin samun abinci.
A cikinsu, mutum 637,000 suna fuskantar yunwa mai tsanani, wanda matakinsa ya fi na ko ina a duniya.
Yara sun fi rauni a lamarin, inda sama da ɗaya cikin uku na yara suke fama da rashin cin abinci mai gina jiki, lamarin da ya zarce kashi 20 cikin 100 da ake amfani da shi wajen ayyana yanayin tamowa.
Hukumar WFP tana gargadin cewa idan ba a samu tallafi ba nan take, ƙasashe biyu masu masauƙin baƙin ‘yan gudun hijira da Sudan kanta za su fuskanci masifa ga mutane, inda za a bar miliyoyin mutane ba tare da abinci ba kuma rashin cin abinci mai gina jiki zai ci gaba da ƙaruwa cikin sauri.