A ranar 29 ga Yuli, a lokacin da majalisar ministocin Birtaniya ta sanar da cewa kasar za ta fara shirin ayyukan amince wa da Kasar Falasdinu, ina tattauna wa ta manhajar Zoom da wani dan Falasdinu da ya yi gudun hijira da ya yi karatun shari’a.
Idanunta sun kumbura, muryarta a hade amma ta yi nauyi. Sa'o'i kadan da suka gabata, an kashe 'yan uwanta su tara, da suka hada da yara, a wani harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai a sabon sansanin ‘yan gudun hijira da ke Nuseirat.
Ba wai tana neman a tausaya mata ba ne. Juriyarta ta kai matukar kurewa; ta koma yin rubuce-rubucen irin azabtarwa da raba jama'a da matsugunansu ga kunshin bayanan shigar da kara gaban shari’a da muke tattarawa, kuma ta yi shiru tana tambayar, "Shin duniya na bukatar kasar Falasdinu idan babu Falasdinawa da suka rage da za su zauna a cikin ta?"
Yayin da Biritaniya ta saka sharadin tsagaita wuta ko ta amince da Falasdinu, wasu kasashe irin su - Faransa, Spaniya, da Ireland - sun tabbatar da nasu kudirin, kuma a ranar 30 ga Yuli, Kanada ta bayyana aniyar ta ta bin sahu. An yaba da wannan a matsayi na sauyin diflomasiyya.
Amma Falasdinawa sun san wasan kwaikwayon sosai: amincewa da da ake yi ba adalci ba ne, munafurci ne.
Kanada, kamar yadda ta yi alƙawarin amincewa, ta ci gaba da ba wa Isra'ila makamai. Birtaniya ta yi kira ga daukar mataki a kasar, yayin da har yanzu ta ki dakatar da fitar da makamai zuwa Isra’ila.
Ga duka bangrori biyun, batun amincewa da kasa ba shi kimar kare mutuncinsa da zama masu neman fake wa kawai, wanda hakan ke kare su daga bayyana gaskiya a yayin da suke ci gaba da taimaka wa yakin na Isra’ila.
Waɗannan maganganun, waɗanda aka tsara a matsayin wani ɓangare na babban yunƙurin Turai, an bayar da su matsayin shaidar cewa 'maslahar kafa ƙasashe biyu' na ci gaba da riƙe matsayi na zahiri a cikin tsarin doka, duk da cewar ayyukansa scim ma shirin sun rushe.
Ko da yake, ga Falasdinawa, da ke fuskantar yunwa da Isra'ila ke ci gaba d assasawa a Gaza, da kuma tashe-tashen hankula da 'yan mulkin mallaka ke ta’azzarawa a Yammacin Gabar Kogin Jordan da suka mamaye, irin wadannan alamu ba su da tushe.
Suna tunatar da cewa yayin da Turai ke shelanta amincewa da Falasdinu a matsayin kasa, ba sa bayar da kariya ga mutanen yankin da ake kawarwa daga ban kasa.
Ga Falasdinawa, gaskiyar abin da ke faruwa a bayyane take.
Tun daga ranar 7 ga Oktoban 2023, Gaza ta kasance wurin da Isra'ila ta tilastawa jama'a shiga hatsarin yunwa, da yin ruwan bama-bamai, da kuma kashe fararen hula, yayin da Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye ya tarwatse saboda shirin fadada matsugunan ’yan kama guri zauna da hare-haren soji.
Dadaddun manufofin mamaya na Birtaniya a Falasdinu sun sanya ba mamakin ganin irin matsayin da ta dauka a yanzu. Yarjejeniyar Balfour ta 1917, da aka fitar ba tare da shawartar Falasdinawa ba, ta bayar da damar kafa Kasar Yahudawa a yankin da ba nasu ba.
Fiye da ƙarni guda bayan haka, Birtaniya a yanzu ta nuna amincewa bisa sharadi ga al'umar Falasdinu, amma fa sai idan Isra'ila ba ta dakatar da yaƙin ba.
Tsarin bayar da izini yana ci gaba da gudana ta hanya ɗaya ne kawai: daga mai mulkin mallaka zuwa wanda ake yi wa mulkin mallaka, daga dan mamaya zuwa wanda aka mamaye.
To, tambayar ba ita ce ko Falasdinu ta cancanci samun matsayin kasa ba, a'a, ko kasashen duniya za su dunkule kalamansu su dace da ayyukansu da ke baiwa kasa ma'anarta ta kasa.
Akwai kasar Falasdinu - doka ta riga ta yi magana
Amincewar London, Paris, ko wani babban birni ba ya nuna Falasdinu ta samu wajen zama; kawai hakan na sake bayyana abinda dokokin kasa da kasa suka tabbatar ne.
Yarjejeniyar Montevideo ta bayyana sharuɗɗa da manufofi huɗu don zama kasa: yawan dauwamammun jama'a, bayyanannun iyakoki, gwamnati mai aiki, da ikon shiga cikin harkoki da huldar ƙasa da ƙasa. Falasdinu na da dukkan wadannan abubuwa hudu.
Kamar yadda Marigayi James Crawford ya fada a cikin rubutun ‘Ƙirƙirar Jihohi a Dokokin Ƙasashen Duniya’, "mamaya ko takaddamar iyakoki ba ya hana a kafa kasa”…..ana kafa kasa da shruddan manufofi ba wai da cikar ‘yancin mulki ba.
Tun bayan shelanta 'yancin kan Falasdinawa a 1988, fiye da kasashe 140, daga Kudancin Duniya, sun amince da Falasdinu a hukumance.
Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da ita a matsayin kasa mamba ‘yar kallo, aka ba ta damar shiga yarjeniyoyin kasa da kasa da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya.
Kotun kasa da kasa, a cikin Shawarwarinta Bisa Ra’ayi na 2004 kan gina katangar raba yanki da Isra'ila ke yi, ta bayyana cewa: 'yancin Falasdinawa na cin gashin kai al'ada ce, wadda dukkan kasashe ke tafiya a kai, kuma ba za a iya dakatar da su ta hanyar mamaya, hadewa, ko "tattaunawa" ba.
A 2024, Alƙali Gomez Robledo, a ra'ayinsa na daban kan wannan batu da yake gaban shari’a, ya yi gargaɗin da ake ganin ya dace da abubuwan da ke afkuwa a yau.
Ya yi gargadin cewa kar a bari amincewa ta zama madadin daukar kwararan matakan kawo akrshen mamaya” ko a bari hakan ya zama wata faka ta jinkirta samun cikakken ‘yancin mulki na Falasdinawa.
Duk da haka, wannan ne ainihin hatsarin da matakan kasashen yammacin duniya ke haifarwa: kalaman da ke kawo batun kafa kasa a matsayin al’ada, na aiki don tabbatar da mamayar da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa, maimakon kalubalantar hakan.
Idan har ba za a aiwatar da su ba, to takunkumai, matakan shari’a da kwararan matakan ruguza mamaya, na kawo hatsari ga matsayin halasci, wanda aka gina kan yunwatarwa, rushe matsugunai, da abinda kwararrun MDD a yanzu ke kira da nuna wariya da kisan kiyashi.
Amince wa ba tare da aiwatarwa ba na janyo karo da juna
Idan babu aiwatarwa, ayyana kafa kasar Falasdinawa, ko daga Turai ko kuma wani wuri, zai zama marar wani tasiri in banda ayyukan diflomasiyya kawai.
Suna kwantar da hankulan kasashen duniya yayin da suke barin Falasdinawa cikin gwagwarmayar rasa matsugunai da kararwa. Ana yi wa wadannan matakan farfado da maslahar kafa kasashe biyu.
Sai dai kuma, wannan tsarin ya zama marar amfani ta hanyar matakan da aka dauka da gangan.
Firaminista Benjamin Netanyahu ya fada a fili a karshen 2024, "A karkashin kulawata, ba za a taba kafa kasar Falasdinu ba."
Ministan Kudi Bezalel Smotrich, mai tsara fadada matsugunan Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, ya sha maimaita wannan kalamin: "Babu al'ummar Falasdinu; ƙasar tamu ce mu kaɗai."
Waɗannan ba tsokana ba ce boyayyiya; su ne akidun da ke jagorantar kasar da ke ci gaba da mamayar matsugunan Falasdinawa, lalata iyakokin da mayar da manufofin cinye yankunansu ba komai ba.
Amincewar da ta gaza aiki da iyakokin 1967, kamar yadda Hukunci na 2334 na Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniyya ya wajabta, kasa tabbatar da kan iyakokin 1967, kamar yadda kudurin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2334 ya wajabta, bai kalubalanci wannan ba, kara karfafa mas agwiwa ma ya yi.
Kotun Kasa da Kasa, Majalisar Dinkin Duniya, da Yarjejeniyar Geneva sun wajabta wa kasashe ba wai kawai su kauracewa amincewa da haramtattun yanayi ba, har ma da daukar matakin kawo karshen su ta hanyar takunkumi, takunkumin hana mallakar makamai, aiwatar da sammacin ICC, da matakan hadin kai don lalata mamaya.
Falasdinawa ba sa buƙatar wani “tsari” marar tushe, wata sabuwar amincewa tare da bikin da aka naɗe da lafazin ƙasashen yamma.
Suna buƙatar amincewa da matakan da za su biyo baya za su karfafa: kawar da yankunan da aka mamaye da janye kawanyar da aka yi musu, sannan a hukunta wadanda ke da hannu a kotunan kasa da kasa, sannan a hada hannu waje guda don dakatar da ayyukan kisan kare dangi.
Idan ba tare da wannan ba, amincewar ta zama wani takunkumin fuska, wasan kwaikwayon da ke ayyana matsayin kasa a waje a yayin da Falasdinawa ke fuskantar yunwar dole, gudun hijira, da binne su a gidaje.
Har sai kasashe sun mayar da kalamansu sun koma bayar da kariya, hukunta masu laifi, da adalci, duk wani furuci zai zama abinda Falasdinawa suka riga suka sani: sanarwar bayan taro ga manema labarai, ba wai mataki ba.