DUNIYA
2 minti karatu
Rasha ta zama ƙasa ta farko da ta amince da gwamnatin Taliban a Afghanistan
Ma'aikatar Harkokin Waje ta Rasha ta ce, hakan zai buɗe hanyar "haɗin kai na diflomasiyya mai alfanu a tsakanin ƙasashen biyu" a ɓangarori da dama.
Rasha ta zama ƙasa ta farko da ta amince da gwamnatin Taliban a Afghanistan
FILE PHOTO: Members of the Taliban delegation during international talks on Afghanistan in Moscow, Russia. / Reuters
3 Yuli 2025

Rasha ta bayyana cewa ta karɓi takardun shaidar kama aikin sabon jakadan Afghanistan, wanda hakan ya sa ta zama ƙasa ta farko da ta amince da gwamnatin Taliban a ƙasar.

“Mun yi imani cewa wannan matakin na amincewa a hukumance da gwamnatin Daular Musulunci ta Afghanistan zai ba da damar haɓaka haɗin gwiwa mai amfani tsakanin ƙasashenmu a fannoni daban-daban,” in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Afghanistan ta tabbatar da wannan ci-gaban, tana mai cewa jakadan Rasha Dmitry Zhirnov ya gana da Ministan Harkokin Wajen Taliban Amir Khan Muttaqi, inda ya isar da wannan matakin na gwamnatin Rasha da ke nuna “muhimmancin wannan mataki”.

Zhirnov ya bayyana wannan a matsayin “mataki mai tarihi wajen ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.”

Ma’aikatar Harkokin Wajen Afghanistan ta ce: “Da wannan mataki, dangantakar ƙasashen biyu za ta ƙara faɗaɗa.”

Muttaqi ya nuna fatan cewa wannan zai haifar da ƙarin haɗin gwiwa da kuma ƙarfafa dangantaka tsakanin Afghanistan da Rasha.

Zhirnov ya shaida wa tashar talabijin ta gwamnati Rossiya-1 Shugaba Vladimir Putin ne ya ɗauki wannan matakin bisa shawarar Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov. “Wannan yana nuna burin gaskiya na Rasha na kafa haɗin gwiwa mai ƙarfi da Afghanistan,” in ji shi.

Rasha ta zama ƙasa ta farko da ta amince da gwamnatin Taliban a hukumance.

Babu wata ƙasa mamba a Majalisar Ɗinkin Duniya da ta amince da gwamnatin rikon ƙwarya ta Taliban tun dawowarta kan mulki a watan Agustan 2021.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us