Manyan ‘yan jam’iyyar adawa a Nijeriya sun fara mayar da martani bayan da hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon ƙasa ta tsare tsohon gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal bisa zargin saɓa dokokin kuɗi.
Tun da fari jaridun ƙasar ne suka ambato majiyoyi daga EFCC suna cewa an riƙe tsohon gwamnan a hedikwatar hukumar da ke Abuja ranar Litinin kan zargin cire naira biliyan 189 ba bisa ƙa’ida ba.
Sai dai a ranar Talata da safe, sai tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya, kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa a PDP a 2023, Atiku Abubakar, ya wallafa a shafinsa na X cewa, EFCC ta kama Tambuwal ne kawai saboda shi ɗan jam’iyyar adawa ne.
Atiku, wanda a yanzu yake sabuwar jam’iyyar adawa ta haɗaka a Nijeriya wato ADC, inda suke tare da Tambuwal, ya ce “dalilin da ya sa EFCC ta tsare tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, shi ne saboda yana cikin jam'iyyar adawa ta haɗaka. Wannan na nuna yadda gwamnatin Tinubu ke ci gaba da yaɗa manufofinta na musgunawa da tsoratarwa, da rusa ’yan adawa.”
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ƙara da cewa “A yau dai duk wanda yake da alaka da ‘yan adawa to za a zarge shi da cin hanci da rashawa, kuma da zarar an tilasta musushiga ajandar siyasar Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu, to sai ya zama kamar an gafarta musu zunuban su ne.”
PDP ma ta soki lamarin
Ita ma Jam’iyyar adawa ta PDP reshen Jihar Sokoto, a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, ta ce kama tsohon gwamnan Jihar na cike da siyasa.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Jam'iyyar PDP na Jihar, Hassan Sahabi Sanyinnawal ya fitar ya ce kama Tambuwal wani yunƙuri ne na rufe bakin jam'iyyun adawa da tsorata su a ƙasar.
Kan batun tsare Tambuwal ɗin kuwa, wasu jaridun ƙasar sun ruwaito cewar hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan wanda ya taɓa zama shugaban majalisar wakilan ƙasar ne kan yadda ya cire kuɗaɗen daga banki abin da ya saɓa wa dokar haramta sama-da-faɗi da kuɗi ta 2022.
Sai dai wasu rahotanni sun ambato majiyoyi daga hukumar na cewa gayyatar Tambuwal kawai hukumar ta yi, ba kama shi ba ne.
Majiyoyin na cewa an gayyace shi ne domin ya yi ƙarin haske game da naira biliyan 189 da ake zargin ya cire ba bisa ƙa’ida ba.
Amma a gefe guda, wasu rahotanni sun ce EFCC ta gayyaci Emeka Ihedioha, tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilan Nijeriya a lokacin da Tambuwal yake Shugaban Majalisar.
Kazalika rahotannin sun ce ana sa rai Ihedioha wanda tsohon gwamna ne na Jihar Imo zai amsa gayyatar da aka yi masa cikin mako ɗaya.
Aminu Waziri Tambuwal dai yana cikin ‘yan siyasar da suka kafa Jam’iyyar APC.
Sai dai kuma daga baya ya sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar PDP, kuma daga bisani ya shiga cikin Jam’iyyar haɗaka ta ADC da ke ƙoƙarin karɓe mulki daga hannun Jam’iyyar APC tasu Shugaba Bola Tinubu.