Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yaba wa Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima a wani saƙo na bikin cikarsa shekara 59 da haihuwa, inda ya bayyana shi matsayin “abokin aiki” mai aminci wanda mutum zai iya yarda da shi a ƙoƙarin gina ƙasa mai wadata.
Ya ce sadaukarwar da Shettima yake yi wajen ganin an samu ci-gaba a Nijeriya ta tabbatar masa cewa bai yi kuskure ba wajen ɗaukarsa a matsayin mataimakinsa.
Wannan na cikin wata sanarwa da shugaban ƙasar ya fitar kuma kakakinsa, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafinsa na X.
“A yau, 2 ga watan Satumba shekarar 2025, ta ba ni wata damar taya ka murna, ɗan’uwana abokin aikina kuma mataimakin shugaban ƙasa yayin da ranar haihuwarka ta zagayo,” in ji saƙon na Tinubu.
Ya yaba da jarumta da juriyar Shettima tun lokacin da ya haɗa kai da shi a kan hanyar sake wa ƙasar fasali.
“Tun da muka fara wannan tafiya, wadda hangen nesa na gina ƙasa mai wadata ya haɗa mu, jarumtarka da sanin ya kamata, da jajircewa da azama da yarda da girman Nijeriya bai taɓa kasancewa cikin shakka ba.
“Ka yi wa mutanen Borno, Jiharka ta asali, hidima da kyau a matsayin gwamna na shekara takwas kuma daga bisani ka yi Sanata mai wakiltar Borno ta Tsakiya a majalisar dattawa.
“A muƙaman biyu, ka nuna cewa shugabanci hidima ne, ba gata ba ne, duk da ƙalubale mai yawa,” a cewar shugaban.
“Duk da haka, hidimarka ga Nijeriya, wanda sha’awarka ga dimokraɗiyya gwamnati mai aiki da cigaban tattalin arziki, sun futo sosai” in ji shugaba Tinubu.
Shugaban ya kuma bayyana godiyarsa ga goyon bayan Shettima da yake samu tare da yin aiki da shi a gwamnati.
“Sadaukarwar da kake yi tana ƙara tabbatar mini cewa ban yi kuskure ba wajen ɗaukarka a matsayin mataimakina,” a cewar Shugaba Tinubu.