NIJERIYA
2 minti karatu
Nijeriya ta ƙaddamar da sabuwar manhajar karatu a matakin farko da babbar sakandare da ilimin fasaha
“Sabon tsarin zai kawo daidaito a darussan da ake koyarwa wajen zurfafawa da kuma koyar da ilimi a aikace.
Nijeriya ta ƙaddamar da sabuwar manhajar karatu a matakin farko da babbar sakandare da ilimin fasaha
Daliban firamare a Nijeriya / Unicef
9 awanni baya

Gwamnatin Nijeriya ta kammala nazari mai zurfi kan manhajoji karatu a fannin ilimi a matakin farko da na manyan makarantun sakandire da kuma fannin fasaha, da nufin rage lafta karatu da kuma inganta tsarin koyarwa.

Sabuwar manhajar za ta fara ne a wannan shekarar karatun ta 2025/2026.

Da take sanar da matakin a madadin Ministan Ilimi Dakta Maruf Tunji Alausa, Karamar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sai’d Ahmad, ta ce an gudanar da bitar ne tare da hadin gwiwar Hukumar Bincike da Cigaban Ilimi ta Nijeriya (NERDC), da hukumar ilimin bai-ɗaya a matakin farko Universal Basic Education Council UBEC, da NSSEC, da NBTE, da sauran masu ruwa da tsaki.

“Sabon tsarin zai kawo daidaito a darussan da ake koyarwa wajen zurfafawa da kuma koyar da ilimi a aikace.

“A matakin farko, ɗaliban Firamare na aji 1-3 za su ɗauki darussa 9-10, yayin da wadanda ke Firamare aji 4-6 za su dauki darussa 10-12.

"A Ƙaramar Makarantar Sakandare yawan darussan za su kai 12-14 ne; ɗaliban babbar sakandare za su ɗauki darussa 8-9; makarantun fasaha za su dauki darussan 9-11," in ji ta.

Farfesa Ahmad ta jaddada cewa, manhajojin da aka yi wa kwaskwarima an tsara su ne domin rage yawan abubuwan da ke ciki, da ba da karin lokaci don koyo, da kuma tabbatar da cewa ilimi ya ci gaba da dacewa da abubuwan da suke faruwa a duniya a yau.

Ma’aikatar ta yaba wa masu ruwa da tsaki bisa jajircewar da suka yi tare da ba su tabbacin cewa za a aiwatar da sabbin manhajoji tare da sanya ido sosai don tabbatar da samun karbuwa mai inganci da samun sauyi cikin sauki a makarantu a fadin Nijeriya.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us