SIYASA
2 minti karatu
Ghana ba za ta ci gaba da kashe dala miliyan 15 a ko wace shekara kan hayar ofisoshin jakadanci ba
Shugaba Mahama ya bayyana cewa ya bai wa ministocin harkokin waje da na kuɗi aikin warware wannan matsalar da ta daɗe tana damun ƙasar Ghana.
Ghana ba za ta ci gaba da kashe dala miliyan 15 a ko wace shekara kan hayar ofisoshin jakadanci ba
Shugaban Ghana John Dramani Mahama / Reuters
7 awanni baya

Shugaba John Dramani Mahama na Ghana ya ce ƙasar ba za ta iya ci gaba da kashe dala miliyan 15 a ko wace shekara domin hayar gidaje da ofisoshin jakadanci ba.

“Hakan ba amfani da kuɗin masu biyan haraji ta hanyar da ta dace ba ne, kuma akwai buƙatar a daina wannan,” kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar Ghana ya ambato shugaban ƙasar yana cewa.   

Shugaba Mahama ya ce wannan shi ya sa majalisar ministocin ƙasar ta amince da shirin STRIDE na dabarun sauyawa daga haya zuwa gina gidajen da ƙasar za ta yi amfani da su a ƙasashen ƙetare.

Shugaban ya bayyana cewa ya bai wa ministocin harkokin waje da na kuɗi aikin warware wannan matsalar da ta daɗe tana damun ƙasar.

Ya ce daga bayanan da aka ba shi a baya bayan nan, ya fahimci cewa an riga an naɗa mai ba da shawara game da kashe kuɗi kuma ana zanen gine-ginen yayin da ake tattaunawa game da yadda za a samu kuɗaɗen gina su.

Shugaban Ghana ya jaddada cewa wannan dabarar za ta sa ma’aikatan ofishoshin jakadancin Ghana a ƙetare su riƙa zama a gidaje mallakar ƙasar, lamarin da zai sa rage almubazaranci tare da kare mutuncin ƙasar a duniya.

Shugaba Mahama ya tuna wa jakadun ƙasar a ƙetare cewa hakan aikin kowane ɗan ƙasar ne kuma nasararta ta dogara ne ga haɗin kai tsakanin ofisoshin jakadancin ƙasar a ƙetare da ma’aikatar harkokin wajen ƙasar da ma’aikatu da ofisoshi da hukumomin gwamnati.

“Yayin da kuka kama wannan aikin, ku tuna cewa aikinku ba naku kaɗai ba ne, aiki ne ga ƙasarku da Allah. Ku yi hidima cikin tawali’u da ƙarfin hali da inganci. Allah Ya sa wa’adin aikinku ya bai wa Ghana sa’a, ci-gaba ga mutanenmu da kuma mutunci ga ko wane ɗan Ghana a gida da ƙetare,” in ji shuguban.

Da yake mayar da martani a madadin sabbin jakadun ƙasar a ƙetare, sabon jakadan Ghana zuwa ƙasar Amurka, Mista Victor Emmanuel Smith, ya gode wa shugaban ƙasar game da girmamawar da aka yi musu kuma ya nemi abokan aikinsa su mayar da hankali kan manufofin shugaban ƙasar.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us