SIYASA
2 minti karatu
Dakarun tsaron Nijar sun daƙile hari a Abalama sun kashe ‘yan bindiga
An kashe biyu daga cikin maharan yayin da aka kama uku daga cikinsu inda ɗaya daga cikin dakarun tsaron ƙasar ya rasu kuma huɗu daga cikinsu suka raunata.
Dakarun tsaron Nijar sun daƙile hari a Abalama sun kashe ‘yan bindiga
Dakarun tsaron ƙasar Nijar sun yi nasarar kashe biyu daga cikin maharan / Actu Niger
14 awanni baya

Dakarun tsaron Jamhuriyar Nijar sun yi nasarar daƙile hare-hare biyu da ‘yan bindiga suka yi yunƙurin kai wa a sansanonin dakarun tsaron ƙasar da ke garin Abalama a gundumar Aderbissanat.

Kafar watsa labarai ta Actu Nijar ta ruwaito cewa ranar Alhamis ne aka yi bikin gabatar da makaman da dakarun suka ƙwace daga maharan wanda gwamnan yankin Manjo Janar Ibra Boulama Issa, ya halarta.

Sai dai ta ce abin takaici shi ne soja ɗaya ya rasu sannan huɗu sun jikkata a fafatawar da dakarun suka yi da ‘yan bindigar a ranar Talata, ko da yake su ma sojoji sun kashe ‘yan bindiga biyu.

Haka kuma an kama uku daga cikin maharan, yayin da wasu suka tsere ɗauke da muggan raunuka.

Bikin, wanda aka yi a sansanin dakarun tsaron ƙasa na Agadez, ya haɗa jami’ai na farar-hula da soji ciki har da shugaban gundumar Aderbissanat, wanda bai jima da dawowa daga bin maharan ba, da mataimakin shugaban gundumar Agadez da kuma kwamandan bataliya Assarid Almoustapha.

Makaman da aka gabatar a bikin sun haɗa da rokokin RPG huɗu  da bindigogi ƙirar AK-47 huɗu da rokoki uku da RPG7 biyu da gidan harsasai uku da sauransu.

Kazalika ababen sun haɗa da wayar salula ƙirar Motorola da kuma wata mota ƙirar Tondra.

Hare-haren da aka kai kan sansanonin dakarun tsaron ƙasar a lokaci ɗaya an daƙile su ne bisa jajircewar dakarun tsaron ƙasar.

Shugaban gundumar Aderbissanat ya yaba wa ƙarfin halin da dakarun tsaron ƙasar Nijar suka nuna a lokacin daƙile hare-haren.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us