DUNIYA
3 minti karatu
Kremlin ta yi watsi da kalaman Trump cewa Sin, Koriya ta Arewa, da Rasha suna ƙulla wa Amurka tuggu
"Babu wani daga cikin waɗannan shugabannin uku da yake da wannan aniyar a ransa," a cewar wani mai taimaki wa Shugaban Rasha, Yuri Ushakov, yana mai cewa duka suna fahimtar rawar da gwamnatin Amurka ke takawa a wannan yanayi da duniya ke ciki.
Kremlin ta yi watsi da kalaman Trump cewa Sin, Koriya ta Arewa, da Rasha suna ƙulla wa Amurka tuggu
Vladimir Putin, Xi Jinping, da kuma Kim Jong Un sun halarci faretin soja don tunawa da cika shekaru 80 da mika wuyan Japan a yakin duniya na biyu / AP
3 Satumba 2025

Moscow ta musanta zargin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa shugabannin Rasha da China, da Koriya ta Arewa suna haɗa kai don ƙulla wa Washington maƙarƙashiya a daidai lokacin da aka gudanar da wani gagarumin faretin sojoji a Dandalin Tiananmen na Beijing.

“Ina so in ce babu wanda yake ƙulla wa Amurka tuggu, babu wanda ya shirya wani abu, babu wata maƙarƙashiya. Haka ma, babu wanda ya yi tunanin hakan; babu wani daga cikin wadannan shugabanni uku da ya yi hakan,” in ji wani mai ba da shawara ga Shugaban Ƙasar Rasha, Yuri Ushakov, a wata hira da ya yi da dan jaridar Rasha Pavel Zarubin, wadda aka wallafa a shafinsa na Telegram a ranar Laraba.

Maganganun Ushakov sun biyo bayan wani gagarumin fareti da kasar China ta shirya don tunawa da cika shekaru 80 da nasarar da aka samu kan Japan a yakin duniya na biyu, wanda shugabannin kasashen waje da dama suka halarta, ciki har da Shugaban Rasha Vladimir Putin, Shugaban China Xi Jinping, da Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un.

Beijing tana kiran lokacin 1937-1945 da suna "Yakin Gwajin Kare Kai daga Mamayar Japan" kuma tana daukar sa a matsayin wani muhimmin bangare na "Yakin Duniya na Adawa da Kama-karya."

“Bugu da ƙari, zan iya cewa kowa yana fahimtar irin rawar da Amurka, gwamnatin yanzu ta Shugaba Trump, da Shugaba Trump kansa ke takawa a halin da ake ciki a duniya,” in ji Ushakov, yana mai cewa yana ganin maganganun Trump ba su rasa wani nau’i na barkwanci ba.

A cikin wata hira da ya yi daga baya da manema labarai, mai magana da yawun Kremlin Dmitry Peskov ya kuma yi tsokaci kan furucin Trump, yana fatan cewa kalaman Shugaban Amurka sun kasance cikin wata ma’ana ta alamar misali, musamman ma tun da babu wanda ke yin wani shiri.

Ya kara da cewa dangantakar Rasha da abokanta na gabas, musamman China da Koriya ta Arewa, a cikin tsarin hadin gwiwa, ana gudanar da su ne don alheri, ba don yin adawa da wata kasa ba.

Rana guda kfin hakan ne Trump ya zargi Putin da Xi da Kim da yin makarkashiya kan Amurka a wani rubutu da ya wallafa a dandalin sada zumuntarsa, Truth Social, yana mai cewa mutane da dama daga Amurka sun rasa rayukansu a kokarin China na samun nasara a yakin duniya na biyu, kuma yana fatan jarumtaka da sadaukarwarsu za su samu "girmamawa da tunawa daidai gwargwado."

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us