NIJERIYA
3 minti karatu
Ƙoƙarin gwamnatin Nijeriya na sulhunta NUPENG da Dangote ya ci tura
Ƙungiyar NUPENG ta yi shelar cewa za ta fara yajin aiki daga ranar Litinin, 8 ga watan Satumbar shekarar 2025, kan zargin da ta yi wa kamfanin Dangote cewa yana ɗaukar matakan da suka saɓa wa dokokin ƙwadago.
Ƙoƙarin gwamnatin Nijeriya na sulhunta NUPENG da Dangote ya ci tura
Ana ganin yajin aikin ƙungiyar ƙwadago ta NUPENG zai iya haddasa rashin mai a Nijeriya / AA
9 Satumba 2025

Zaman sirrin da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta gudanar ranar Litinin da maraice domin sulhuta ƙungiyar ma’aikatan dakon man fetur da gas (NUPENG) da kamfanin mai na Dangote ya kasa cim ma nasara.


Rahotanni daga Nijeriya sun ce zaman da Ministan Ƙwadagon ƙasar, Mohammed Dingyadi, da Ƙaramar Ministar Ƙwadago, Nkiruka Onyejeocha, suka jagoranta wani mataki ne na warware taƙaddamar da ke tsakanin ɓangarorin biyu domin kauce wa yajin aikin da ƙungiyar NUPENG ta ce za ta yi.

Waɗanda suka halarci zaman sun haɗa da shugabannin ƙungiyar NUPENG da jami’an ƙungiyar ƙwadagon Nijeriya (NLC) da kuma na ƙungiyoyin ƙwadago na TUC.

Kazalika zaman ya samu halartar babban daraktan ajiya da rabawa da sayar da mai na hukumar da ke kula fannin tacewa da sayar da mai ta Nijeriya (NMDPRA), Ogbugo Ukoha, da kuma wakilan kamfanin Dangote da gidan man MRS.

Sai dai an kammala taron ba tare da cim ma matsaya ba game da taƙaddamar da ake yi tsakanin NUPENG da Matatar Mai ta Dangote.

Ranar Juma’ar da ta gabata ne dai ƙungiyar ƙwadagon NUPENG ta yi shelar ƙaddamar da yajin aiki daga ranar 8 ga watan Satumba kan abin da ta kira ƙoƙarin Matatar Man Dangote na hana direbobin tankokin dakon mai na CNG ɗinsa shiga ƙungiyoyin ƙwadago.

Duk da cewa ƙungiyoyin ƙwadagon direbobin tankokin dakon mai na PTD da DTCDA sun nesanta kansu da wannan matakin, NUPENG ta tabbatar ranar Lahadi cewa za ta tsunduma cikin yajin aikin.


Domin ta kauce wa wannan yajin aikin, gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yi kira ga ƙungiyar ƙwadagon ranar Lahadi ta sake tunani kan wannan matakin nata.

Dingyadi, a wata sanarwar da shugabar sashen sadarwa ta ma’aikatarsa, Patience Onuobia, ta fitar, ya yi kira ga NUPENG ta dakatar da yajin aikinta domin ba da damar tattaunawa.

Ministan na Ƙwadago ya kuma yi kira ga NLC ta janye shawarar da ta bai wa ƙungiyoyin da take da alaƙa da su na kasancewa cikin shirin shiga yajin aikin goyon bayan NUPENG kan abin da ta kira “matakan ƙin jinin ma’aikata da ƙungiyoyin ƙwadago” na kamfanin Dangote.

Ministan ya ce, “na kira duk masu ruwa da tsaki domin wani zaman sasantawa ranar Litinin 8 ga watan Satumba na shekarar, 2025. Tun da na riga na sa baki, na roƙi NUPENG ta janye matakin da ta ɗauka na rufe fannin man fetur daga gobe” .

“Fannin man fetur na da humimmi ga wannan ƙasar. Ya ƙunshi asalin tattalin arziƙin ƙasar. Yajin aiki , ko na rana ɗaya ne, zai yi tasiri mai muni, da zai janyo asarar biliyoyin naira da kuma wahala mai tsanani ga ‘yan Nijeriya,” in ji ministan.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us