Bikin Wasannin Al’adu Karo na 7 ya farfado da hadin kan al’adu, iyalai da ma duniya
Bikin Wasannin Al’adu Karo na 7 ya farfado da hadin kan al’adu, iyalai da ma duniya
Bikin ya tattara mutane sama da 1,000 daga kasashen duniya 35, inda suka mauar da Filin Jiragen Sama na Ataturk da ke Istanbul zama wajen raya al’adu da dabbaka wasannin gargajiya.
2 Yuli 2025

Tutoci sun yi ta kadawa, sahun tafiyar kofaton dawaki sun dinga amo a kan kwaltar filin jirgin saman Ataturk na Istanbul a wannan makon, a yyin bikin raya al'adun al’ummu karo na 7. An bude taron tare da wani shagali mai kayatarwa na wasannin dauri , kade-kade, da kuma mutuntajar bai daya.

Bikin da Tarayyar Wasannin Kabilu (WEC) ke shiryawa zai dauki tsawon kwanaki hudu daga 22 ga Mayu zuwa 25 ga Mayu, ya tattara ‘yan wasa 10,000 daga kasashen duniya 35 don girmama al’adun d akowa ke takama da su.

Taken bikin na bana shi ne Al'ada na farawa a cikin iyali ya yi daidai da ayyana shekarar 2025 da Shekarar Irar Iyali da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yi.

Ta hanyar wasan kwaikwayo, tarurrukan mu'amala, da nuna al'adu, bikin ya zama cikakkiyar shaidar yadda dabi'u da suka samo asali a cikin tarihi za su ci gaba a duniya mai saurin zamanantuwa.

A jawabinsa na bude taron, shugaban kungiyar wannin al’adun al’umma ta duniya Bilal Erdogan, ya bayyana babbar manufar bikin, inda ya jaddada cewa kiyaye al'adu da kayan al’adu nauyi ne a kan duniya baki daya.

"Muna farin cikin ganin irin wannan nuna tsananin sha’awar shirin daga jama'a a musamman a rana ta farko. Wannan tabbaci ne cewa matasa masu tasowa suna da burin alakantuwa da al'adunsu.

“Wannan bikin ba wai kawai girmamawa ga abin da ya gabata ba ne, gada ce ta zuwa gaba da makoma. Idan muka yi nasarar cigabantar da dabi'un da suka mayar da waɗannan ƙasashe namu suka zama gidajenmu, to za su ci gaba da kasancewa mahaifarmu na tsawon wasu shekaru dubu.

“Lallai kar mu sake mu rasa wannan daraja. Ina mika godiya ga dukkan wadanda suka bayar da gudunmawa.”

Erdogan ya kuma tabo batun yanayin jin kai kan bayyana al'adu, yana mai nuna mahimmancin wasanni ga yara a duniya:

"Kowane yaro yana da 'yancin yin wasa, amma yara da yawa, musamman a wurare irin su Gaza, na rasa wannan haƙƙin.

“Wannan bikin kuma mataki ne na inganta ɗabi'a, taro na hankali da aiki da kwakwalwa, inda muke kira ga samar da duniyar da yara ke dariya a cikin ta, ba a ɓoye a ƙarƙashin buraguzai ba."

An ƙaddamar da Tarayyar a 2015 a Kyrgyzstan, Tarayyar wasannin kabilun a’umma na d amambobi 42 a kasashn duniya 27 inda suke kuma shirin da shirin kai wa ga kasashe 60 a shekaru biyar masu zuwa.

Kira ga dorewar al'adu

Bikin na wannan shekara na nuna nau'ikan wasanni na gargajiya-daga harba kwari da baka a kan dawaki, da kokawa, zuwa wasanni masu aiki da lokaci, irin su wasannin Turkawa na Mangala da 19 Tas.

Amma wasannin sun wuce batun tuna baya, suna kuma gabatar da kan su a matsayin martani na zamani ga yawaitar amfani da wayar hannu da dangoginta a tsakanin matasa.

Osman Askin Bak, Ministan Matasa da Wasanni na Turkiyya, wanda ya bi sahun Erdogan wajen halartar bikin, ya yaba wa taron saboda jawo hankalin matasa da yake yi.

“Ganin yaranmu da matasanmu sun rungumi wannan biki yana sanya mana fata mai kyau. Al'adu na daya daga cikin jigon dabi'un al'ummarmu.

Muna godiya ga Ƙungiyar Raya Al’adun Al’ummu ta Duniya saboda kare waɗannan al'adun tare da raya su. Tare da goyon bayan shugabanmu, muna gina al’umma mai karfi da ke da asali. Wasanni, al’adu, da asalin al’adu - duk suna tafiya tare.”

Ya kara da cewa: "Ba za mu manta da Gaza ba. Kar mu yi shiru yayin da ake kashe yara. Bari mu daga murya don smaar da duniyar da kowane yaro zai yi wasa a cikin ta."

Cakuduwar tunani da kamanni

Daga cikin masu halartar biki akwai Ayse Nur Menekse, wata mai bincike kuma marubuciya.

"Wadannan ba wasanni ne kawai da aka gada ba - cakuduwar kamanni da asali ce,” ta fada wa TRT World.

"Bikin ya zama kamar wata gada ta al'ada wacce ta tashi daga abubuwan da suka gabata zuwa makomarmu. A zamanin da muke tsoron rasa tushenmu zuwa yanar gizo, wannan matakin farfaɗowa ne da ya samo asali." in ji ta.

Ta kara da cewa, “Kallon yadda kasashe daban-daban suke yin wasa kafada da kafada—kayatarwa, raba kayayyakinsu, dariya tare—ya burge ni sosai.

A yayin da nake ratsa tantunan Kyrgyzstan da Kazakhstan, na yi tunanin ni ma ga ni a kan tudu hannu da hannu tare da ’yan’uwanmu maza da mata na Asiya ta Tsakiya. Lokaci ne da ya cancanci a shaida ganin sa.”

A ko'ina cikin filin bikin, baƙi sun tsyaa suna kallon harba kwari da baka a kan dawaki, kokawa, da sukuwa. Yara na sauraron almara ind amatasa ke dandana abinci kala-kala daga sassan duniya.

Wani sabon abun dubawa a wannan shekara shi ne "Family Oba", wuri mai na musamman da inda iyalai ke yin sana'a, suna sauraron wakokin zamanin baya, da wasannin da ke ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin al’ummu.

A yayin da dawakan Karabakh suka firgita ’yan kallo tare da kai komon su masu ban sha’awa, kuma kamar yadda waƙoƙin da aka dakko, bikin ya kayatar sosai. Ba wai kare al’adu kawai yake yi ba, har ma da ba su damar shakar numfashi da girmama.

"Kowane tanti yana ba da labari," in ji Ayse Nur Menekse. "Kowace waƙa na ɗauke da asali da kamanni. Kowane wasa na bayyana wata daraja."

Ga marubuciya Melike Gunyuz, wannan ne karo na farko d ata halarci bikin yayin da ta bar ra'ayi mai gamsarwa a a tattaunawarta da TRT World.

"Yanayin ya kasance mai ban sha'awa," in ji ta, muryarta ta bayyana jin daɗinta. "Tawagar Karabakh daga Azerbaijan ta kasance mai ban sha'awa da kayatarwa - tana cike da mawaka da makada, marayan gargajiya da masu wasannin zmaani suna ta cashewa tare. Abin da ya fi ba ni mamaki yadda daga cikin su har da mata.”

A wajen Gunyuz, babban sakon d aake dauka na da sauƙi, amma kuma mai zurfi ne: "Na ci gaba da tambayar kaina: Me ya sa ban taɓa zuwa nan ba? Kowane yaro da kowane matashi ya kamata su shaida wannan biki. Ba kawai taro ba ne - yana nishadantar da mahalarta.

Kasancewar sa har zuwa 25 ga Mayu tare da bayar da damar shiga kallo kyauta, bikin Wasan al’adun Kabilun na bakwai, yana gayyatar jama'a don shaida al'ada a cikin motsi: dandano, ji, da kuma ruhun al'ada.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us