’Yan ta’adda na Boko Haram sun kashe aƙalla mutum 63 a wani gari na arewa maso gabashin Nijeriya yayin da suka far ma garin da aka mayar da mutanensa daga sansanin ‘yan gudun hijira, in ji gwamnan jihar.
An kai harin ne ranar Juma’a da daddare a garin Darul Jamal, wanda ke da sansanin soji a kan iyakar Nijeriya da Kamaru.
Babagana Zulum, gwamnan Jihar Borno da ke fuskantar ƙalubalen tsaro, ya ce sojoji biyar na cikin waɗanda suka mutu, adadin da wata majiyar tsaro ta tabbatar wa kamfanin dillancin labaran AFP.
"Abin takaici ne, an sake tsugunar da wannan al’ummar ne cikin watannin da suka wuce kuma sun ci gaba da lamuransu na yau da kullum," kamar yadda Zulum ya sanar da ‘yan jarida a wurin da aka kai harin.
'Ihu da harbin kan mai-uwa-da-wabi'
"Kawo yanzu, mun tabbatar da rasuwar mutum 63, ciki har da fararen-hula da sojoji."
Mazauna garin sun ce an fara harin ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare (ƙarfe 7:30 agogon GMT), lokacin da gomman mayaƙa suka iso bisa babura suna harbi da kuma ƙona gidaje.
"Sun zo suna ihu kuma suna harbin kan mai-uwa-da-wabi," kamar yadda Malam Bukar, wanda ya tsere da matarsa da ‘ya’ya uku ya shaida wa AFP.
"Da muka dawo da safiya, mun ga gawarwaki sun warwatsu ta ko ina."
Daga farko, kwamandan ‘yan sa-kai na yankin Babagana Ibrahim ya ce an kashe aƙalla mutum 55, yayin da wani ma’aikacin wata ƙungiya mai zaman kanta, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bai wa kamfanin dillancin labaran AFP adadin 64.
Rundunar sojin saman Nijeriya ta ce ta 'kashe ‘yan ta’adda 30 '
A cikin wata sanarwa da kafafen watsa labaran Nijeriya suka wallafa, rundunar sojin saman ƙasar ta ce ta kashe “‘yan ta’adda” 30 waɗanda suka yi musayar wuta da sojojin ƙasa a garin da ake ce wa Dar-El-Jamal.
Yawancin waɗanda lamarin ya rutsa da su iyalai ne da aka mayar gida daga sansanin ‘yan gudun hijira da ke makarantar gwamnatin da ke Bama, wanda aka rufe da farkon wannan shekarar.
‘Yan ta’addan Boko Haram, waɗanda suka fi aika-aika a yankin arewacin Nijeriya, sun shafe shekaru suna ƙaddamar da hare-hare kan fararen hula da jami’an tsaro.