Tun daga zamanin sarakunan kasar China na da da suke neman maganin tsawon rai har zuwa masu bincike na Spain na tsakiyar zamanin da suka yi ƙoƙarin gano marmaron ƙuruciya a nahiyar Amurka, ɗan’adam ya shafe dubban shekaru yana mafarkin tsawaita rayuwa fiye da iyakar ɗabi'a.
A watan Satumba na shekarar 2025, Shugaban Ƙasar China Xi Jinping da Shugaban Rasha Vladimir Putin sun jawo hankalin duniya yayin da aka ji su suna tattaunawa kan batun tsawon rai a wani taron ƙungiyar Shanghai Cooperation Organisation (SCO).
Shugabannin biyu sun yi magana kan ci gaban kimiyya kamar dashen sassan jiki wanda zai iya ninka tsawon rayuwar ɗan’adam har zuwa shekaru 150.
“A baya, ba kasafai ake ganin wanda ya wuce shekara 70 ba, amma yanzu suna cewa ɗan shekara da sauransa sosai,” in ji mai fassara na Shugaban Ƙasar China mai shekaru 72 a cikin harshen Rashanci.
“Hasashen ya nuna cewa, a wannan ƙarni, akwai yiwuwar mutum ya iya rayuwa har zuwa shekara 150,” mai fassarar Xi ya shaida wa Putin.
Amma shin duniya na gab da komawa wajen da ɗan 150 zai zama kamar ɗan shekara 80 ɗin yanzua? Ko kuwa wannan mafarki ne kawai na ɗan’adam da ke neman tserewa mutuwa tun da can?
A cikin 'yan shekarun nan, bincike kan tsawon rai ya koma daga tatsuniya zuwa binciken kimiyya.
Fitaccen mawaki Michael Jackson ya taɓa mafarkin rayuwa har zuwa shekara 150, burin da yanzu ya zama abin sha'awa ga attajiran da ke zuba kuɗaɗe masu yawa a binciken tsufa.
Kamfanoni kamar Calico Labs da Altos Labs, waɗanda Google da Jeff Bezos suka samar, suna jagorantar wannan bincike, inda aka zuba biliyoyin daloli don gano hanyoyin dakatar da tsufa ko rage saurin tsufa.
Wannan ya nuna cewa tsawon rai ba kawai mafarki ba ne yanzu, amma ya zama wani abu da ake bincike a kai da goyon bayan attajirai masu arziki.
Amma tambayar ita ce: Shin mun kusa ganin yadda tsawon rai na shekara 150 ya zama gaskiya?
Wani bincike na shekarar 2024 ya nuna cewa tsawon rai a cikin al'ummomin da suka fi tsawon rai a duniya ya ƙaru da shekaru 6.5 kawai tsakanin 1990 da 2019.
Binciken ya ƙara da cewa kashi 15 cikin 100 na mata da kashi 5 cikin 100 na maza a kowane ƙarni za su iya kaiwa shekara 100 a yawancin ƙasashe a wannan ƙarni, wanda hakan ma yana da wahala.
Duk da haka, masu fata irin su David Sinclair daga Jami'ar Harvard suna ganin cewa sabbin bincike za su iya bai wa yara na yau damar rayuwa fiye da iyakokin yau. “Tsufa cuta ce, kuma wannan cuta tana da magani,” in ji shi.
A cikin shekaru goma da suka gabata, masana kimiyya sun yi manyan nasarori wajen fahimtar dalilin da ya sa ɗan’adam ke tsufa da yadda magunguna za su iya jinkirta mutuwa har na tsawon shekaru.
Wani babban ci-gaba na kimiyya ya kasance a fannin ƙwayoyin halitta (cells) na tsufa, waɗanda su ne sel (cells) da suka daina rarrabuwa kamar yadda ya kamata amma ba su mutu ba.
Wadannan ƙwayoyin halitta suna ci gaba da wanzuwa suna sakin sinadarai masu cutarwa, suna kusantar da mutum ga mutuwa.
Masana kimiyya kwanan nan sun gwada sabbin magunguna a kan ɓeraye waɗanda ke aiki kamar masu tsaftacewa, suna kashe ƙwayoyin halitta marasa lafiya.
Sakamakon ya nuna cewa ɓerayen sun kasance masu lafiya kuma sun rayu tsawon lokaci.
Wani ci gaba kuma ya fito daga wani abu da ake kira epigenetic reprogramming, wanda ya ƙunshi sake farfado da tsoffin ƙwayoyin halitta don su zama kamar sabbi.
Daga 2016 zuwa 2022, gwaje-gwaje da aka yi da wasu sunadarai na musamman da ake kira Yamanaka factors sun sa ɓeraye sun rayu da kashi 20 cikin 100 fiye da yadda aka saba kuma har ma sun dawo da ganin da suka rasa.
A cikin mutane, wani bincike na shekarar 2021 ya nuna cewa cin abinci mai kyau da salon rayuwa mai kyau na iya rage shekarun jiki na mutum da kusan shekaru uku a cikin makonni takwas kacal.
Kayan aiki kamar DNA methylation clocks da aka ƙirƙira a cikin shekaru goma da suka gabata suna ba masana kimiyya damar auna tsawon shekarun jikin mutum, suna taimaka musu gwada waɗannan dabarun rage tsufa daidai.
Haka kuma, akwai ci gaba mai amfani a fannin metabolism, wanda ke da alaƙa da yadda jikinmu ke amfani da makamashi.
An gano wani sinadari mai suna NMN yana ƙara kuzari a cikin sel na ɓeraye, yana sa su rayu tsawon lokaci kuma cikin koshin lafiya. Ana gudanar da gwaje-gwajen mutane yanzu don ganin ko zai yi aiki a gare mu.
Wani maganin tsufa mai suna rapamycin ya sami karɓuwa saboda yana taimaka wa ƙwayoyin halitta su tsaftace kansu daga tarkace, yana jinkirta cututtuka kamar cutar mantuwa ta Alzheimer a cikin ɓeraye kuma yana tsawaita rayuwarsu.
Wani bincike na shekarar 2024 ya nuna cewa hana wani sinadari mai suna IL-11 a cikin ɓeraye ya ƙara tsawon rayuwarsu da kashi 25 cikin 100.
Waɗannan bincike da ci-gaba suna nuna lamarin da ke cike da fata, suna nuna cewa ɗan’adam na iya ƙara shekaru 10 zuwa 20 masu lafiya ga tsawon rayuwarsu.
Amma cim ma tsawon rai na shekara 150 har yanzu kamar mafarki ne mai wahala. Wani bincike, misali, ya yi gargadin cewa kusan ninka tsawon rayuwar ɗan’adam zuwa shekara 150 zai buƙaci ci-gaba na kimiyya da ba za mu iya hango su ba tukuna.
Baya ga kimiyya, al'umma za ta buƙaci yin gyare-gyare masu yawa idan ɗan’adam ya ninka tsawon rayuwarsa.
Yawan jama'a zai iya jefa abubuwa kamar abinci, makamashi, da gidaje cikin matsala.
Haka kuma, idan kawai masu arziki za su iya samun damar magungunan tsawaita rayuwa, hakan zai iya haifar da duniyar da masu arziki ne kaɗai za su iya rayuwa har abada yayin da sauran mutane ba za su iya ba.
Ci gaban kimiyya na shekarun da suka gabata yana nuna cewa ɗan’adam ya fi kusa da samun tsawon rayuwa mai lafiya fiye da kowane lokaci.
A wannan ma'ana, tattaunawar Xi da Putin a taron SCO wani ƙarin haske ne kan makomar da kimiyya za ta sake bayyana iyakokin basirar ɗan’adam.
Sinclair daga Jami'ar Harvard ya ce ɗan’adam ya fi sanin lafiyar motarsa fiye da sanin lafiyarsa. “Wannan abin dariya ne. Kuma hakan zai sauya nan ba da jimawa ba.”