Wani rikicin cacar baka ya ɓarke tsakanin Alaafin na Oyo, Oba Ayoade Akeem Oweye da kuma Ooni na Ile Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi a kan ikon naɗin sarauta a garuruwan Yarabawa.
Rikicin ya ɓarke ne bayan Ooni na Ife ya naɗa wani ɗan kasuwa, Jubril Dotun Sanusi sarautar Okanlomo na ƙasar Yarabawa
Bayan Ooni ya naɗa ɗan kasuwan ne dai Alaafin na Oyo ya bai wa Ooni wa’adin sa’o’i 48 ya janye sarautar yana mai cewa Ooni ba shi da ikon naɗin sarautar da ta shafi ƙasar Yarabawa gaba ɗaya.
Wata sanarwar da sakataren watsa labaran Alaafin na Oyo, Bode Durojaye ya fitar ta ce naɗin da Ooni ya yi na ƙalubalantar ikon Alaafin ne kai tsaye.
Sanarwar ta ƙara da cewa Alaafin na Oyo ne kawai yake da ikon naɗin sarautar da ta shafi duk ƙasar Yarabawa a Nijeriya.
“Kotun Ƙoli kanta ta yanke hukuncin cewa Alaafin ne kawai yake da irin wannan ikon [na naɗin irin wannan sarautar]. Duk da haka, Ooni ya ci gaba da bijire wa doka, yana mai take al’ada da umarnin kotuna,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ce idan Ooni bai janye sarautar cikin sa’o’i 48 ba, zai ga abin da zai biyo baya.
Shi kuwa sakataren watsa labarai na Ooni na Ife, Moses Olafare ya ce Ooni ya hana shi fitar da sanarwa a matsayin martani kan gargaɗin da Alaafin ya yi.
“Shugabana ya ba ni umarnin ka da na fitar da sanarwa kan fankon gargaɗin. Na roƙi gafararku ‘yan jarida masu mutunci,” kamar yadda jaridun ƙasar suka ambato Olafare yana cewe a wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
“Ba za mu iya daraja abin da ba za a iya darajawa ba da martani. Mun bar lamarin wa mutane su ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu a kai kamar yadda suke yi,” in ji shi.
“Bari mu mayar da hankali kan abubuwan da suka haɗa kawunanmu maimakon waɗanda za su iya raba kawunanmu. Babu wata sanarwar. Sai dai sa’o’i ashirin da huɗun kamm!”
Wannan dai ba shi ne karon farko da aka samu irin wannan taƙaddamar tsakanin masarautun biyu ba.
A shekarar 1991 irin wannan taƙaddamar ta kaure a lokacin da marigayi Alaafin, Oba Lamidi Adeyemi ya rubuta wasiƙa ga gwamnan soji na jihar Oyo, Kanar Abdulkareem Adisa, domin sanar da shi game da bijerewar da marigayi Ooni, Oba Okunade Sijuade ya yi wajen naɗa Cif Tom Ikimi a matsayin shugaban jam’iyyar NRC sarautar Akinrogun na ƙasar Yarabawa.
Oba Adeyemi ya bayyana matakin da Oba Sijuade ya ɗauka a matsayin saɓo ga al’adar masarautar, musamman idan aka yi la’akari da cewa irin waɗannan na zuwa daga inda ake tsammanin za a kare tare da ƙawata masarauta da al’ada.
Tuni dai mutane a kafafan watsa labarai suke ta tofa albarkacin bakinsu game da taƙammadar, inda wasu ke ganin Ooni ya fi gaskiya yayin da wasu ke ganin Alaafin ne ya fi gaskiya.
Zuwa lokacin da aka rubuta wannan labarin dai maudu’in Alaafin na cikin ababen da suka fi jan hankali a shafin X a Nijeriya.