NIJERIYA
2 minti karatu
‘Yan bindiga sun kashe mutum 13 a yayin da suke sallah a masallaci a Jihar Katsina
Lamarin ya faru ne a yayin da ake sallar asuba, lokacin da ‘yan bindigar ɗauke da muggan makamai suka dirar wa masallatan tare da buɗe musu.
‘Yan bindiga sun kashe mutum 13 a yayin da suke sallah a masallaci a Jihar Katsina
Gwamnan Jihar Katsina Umaru Dikko Radda / Dikko Radda Facebook
19 Agusta 2025

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a Unguwan Mantau da ke karamar hukumar Malumfashi a jihar Katsina, inda suka kashe masu ibada 13.

Lamarin ya faru ne a yayin da ake sallar asuba, lokacin da ‘yan bindigar ɗauke da muggan makamai suka dirar wa masallatan tare da buɗe musu.

Rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne bayan da a baya bayan nan al’ummar garin suka fatattake su har sau biyu.

Gidan talabijin na Channels TV ya rawaito Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Dr. Nasiru Mu’azu cewa ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa a ranar Talata, inda ya bayyana harin “da na ramuwa da ‘yan bindigar suka kai bayan da a baya mazauna garin suka fatattake su.”

Kwamishina Mu’azu ya ce gwamnatin jihar Katsina tuni ta sanar tura ƙarin tsaro da ɗaukar matakan kariya bayan faruwar mummunan lamarin.

Ya ce a yanzu haka akwai jami’an tsaro jibge a Unguwan Muntau don kwantar da hankula.

“Abin ya faru ne a lokacin da ɓata garin suka ƙaddamar da harin ramuwa a kan al’ummar, Al’ummar Musulmai na salla a masallacin da asuba a lokacin da ‘yan ta’addan suka fara harbin kan mai uwa da wabi a masallacin.

“Harin na ramuwa ne a kan al’ummar, waɗanda suka yi nasarar fatattakar ‘yan bindigar har sau biyu a baya.”

“Mutanen Unguwan Mantau sun ɗauki matakin yin kwanton ɓauna a kan ‘yan bindigan tare da kashe da damansu.

“Sun ceci mutanen da aka sato daga Ruwan Sanyi, da ƙwace Babura uku da bindigar AK-47 biyu. A yanzu haka jami’an tsaro na wajen don dawo da doka da oda a Unguwan Mantau,” in ji kwamishinan.

Kwamishinan ya ci gaba da cewa, tuni aka tura tawagar sojoji da ‘yan sanda domin fatattakar ‘yan bindigar, domin a lokacin damina, ‘yan fashin a cewarsa, suna fakewa a cikin gonaki domin su aikata munanan ayyukansu. 

“Muna kokarin ganin mun kama ‘yan fashin. A matsayinmu na gwamnati, muna jinjina wa al’ummar Unguwar Mantau, kuma mun himmatu wajen yakar wadannan ‘yan bindigar da kuma tabbatar da tsaro a fadin al’ummarmu.

Ya kara da cewa "Gwamnatin jihar tana jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa tare da jaddada goyon bayanta ga shirye-shiryen tsaro na al'umma tare da kokarin kawar da masu aikata laifuka daga yankin," in ji shi.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us