Ko da amincewar Amurka Isra’ila ta kai hare-haren kan taron sulhu a Qatar?
DUNIYA
4 minti karatu
Ko da amincewar Amurka Isra’ila ta kai hare-haren kan taron sulhu a Qatar?Rahotanni da dama daga Isra’ila da kafafen watsa labarai na kasa da kasa na nuni da cewa tare da amincewar Amurka Isra’ila ta kai hari ta sama a Doha, duk da dai Fadar White House ba ta ce komai ba tukunna.
Aftermath of an Israeli attack on Hamas leaders, according to an Israeli official, in Doha / Reuters
11 awanni baya

Sojojin Isra'ila sun kai wani hari kan Qatar, inda suka nufi wata unguwa da ke ɗauke da wasu manyan jami'an Hamas da ke tattauna zaman lafiya.

Harin na nuna sabon matakin da Isra'ila ta dauka na keta hurumin iyaka da ikon wata kasa ta Gabas ta Tsakiya, wanda kafafen yada labaran Isra'ila suka ce ya faru ne da amincewar Amurka.

Qatar, babbar ƙawar Amurka da ke ɗauke da sansanin sojin sama na Al Udeid, nan take ta yi Allah-wadai da "harin da Isra'ila ta kai kan gine-ginen wasu jami'an ofishin siyasa na Hamas a Doha, babban birnin Qatar."

Doha ta tabbatar da cewa ba za ta lamunci "wannan halayya ta rashin hankali ta Isra'ila da kuma yadda take ci gaba da yin katsalandan a harkokin tsaron yankin ba, da kuma duk wani mataki da ya shafi tsaronta da 'yancinta."

Hamas ta ce masu tattaunawar tata suna tattaunawa ne kan tayin tsagaita wuta da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi, wanda Trump ya bayyana a matsayin matakin karshe ga ‘yan gwagwarmayar Falasdinu kafin Isra'ila ta ƙara ƙaimi ga kisan kare dangi a Gaza baki daya.

Hamas ta kuma ce shawarar da Trump ya gabatar wata yaudara ce ta janyo mambobin kungiyar zuwa wani taro don Isra’ila ta kai musu hari.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce majiyoyin Hamas sun shaida musu cewa tawagar da ke tattaunawa kan tsagaita wuta ta tsira daga harin na Isra'ila.

Ofishin jakadancin Amurka da ke Doha ya bayar da umarnin samar da matsuguni ga Amurkawa bayan hare-haren, wanda ke zama martanin farko da Amurka ta mayar a hukumance, ko da yake ba a bayyana kai tsaye kan ko an sanar da jama’a za a kai harin ba.

Rahotanni da dama daga kafafen yada labarai na Isra’ila da na kasa da kasa sun nuna cewa farmakin da Isra’ilan ta bayyana a matsayin “wanda ya nufi inda ake so” da ya hari manyan jami’an Hamas, ciki har da babban mai shiga tsakani Khalil al-Hayya – ya samu hadin kai ko kuma amincewa daga gwamnatin Amurka karkashin Shugaba Trump.

Tashar Channel 12 ta Isra'ila ta bayar da rahoton cewa wani jami'in Isra'ila ya tabbatar da sanar da Washington kafin harin, kuma Trump ya bayar da "izini" don kai harin.

Kafar Middle East Eye ta yi tsokaci da cewa hare-haren da aka kai a Doha an riga an shirya su tare da gwamnatin Amurka.

Ynet News  kuma sun rawaito cewa wani jami'in Isra'ila ya tabbatar da sanar da Amurka kafin kai harin, kuma Trump ya baiwa Isra'ila damar yin hakan.

Kafar yada labarai ta CNN da ke Amurka, ta rawaito wani jami'in Isra'ila ya ce an sanar da Amurka gabanin harin da aka kai wa Qatar.

Netanyahu ya lalata wata damar zaman lafiya?

Masu shiga tsakani na Qatar, Masar da Amurka sun yi ta kokarin ganin an tsagaita wuta na tsawon watanni, amma duk da haka jami'an Isra'ila sun yi watsi da yunkurin dakatar da kisan kare dangi a Gaza da aka yi wa kawanya.

A baya bayan nan kungiyar Hamas ta amince da shawarar tsagaita wuta da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayar, wanda zai sa a sako wasu fursunonin yaki da ake tsare da su a Gaza.

Sai dai Isra'ila da Amurka sun janye bayan Netanyahu ya bukaci a sako mutanen da ake tsare da su gaba daya da kuma Hama ta mika wuya baki daya.

Tun da farko a ranar Lahadin da ta gabata, Trump ya gargadi Hamas da ta amince da sharuddan yarjejeniyar da ya kulla, yana mai cewa: "Isra'ilawa sun amince da sharuddana, lokaci ya yi da Hamas ma za ta amince da su.

Na gargadi Hamas sakamakon rashin amince wa, wannan shi ne gargadina na karshe, ba za a sake samun wani ba!"

Fadar White House ba ta mayar da martani kan harin da Isra'ila ke kaiwa Qatar ba ko kuma ikirarin da kafafen yada labarai ke yi cewa Amurka ta san da za a kai harin.

Sakatariyar Yada Labarai ta Fadar White House Karoline Leavitt za ta yi jawabi ga manema labarai a a ranar Larabar nan.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin Netanyahu ta kira harin da aka kai Qatar "aikin Isra'ila na kashin kanta".

"Isra'ila ce ta shirya kai shi, Isra'ila ce ta gudanar aikata shi, kuma Isra'ila ta dauki nauyin kai shi," in ji ta.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us