SIYASA
3 minti karatu
China za ta karɓi baƙuncin shugabannin ƙasashen duniya a taron SCO don ƙarfafa ikon faɗa-a-ji
Shugabanni daga ƙasashe fiye da 20 za su hallara a birnin Tianjin a daidai lokacin da Shugaba Xi Jinping ke ƙoƙarin amfani da taron ƙolin ƙungiyar SCO wajen ƙarfafa tsaro da tasiri a yankin.
China za ta karɓi baƙuncin shugabannin ƙasashen duniya a taron SCO don ƙarfafa ikon faɗa-a-ji
Shirin Kungiyar Hadin Kai na Shanghai (SCO) / AFP
19 awanni baya

Shugaban ƙasar China Xi Jinping zai karɓi baƙuncin taƙwaransa na ƙasar Rasha Vladimir Putin, da firaministan India Narendra Modi, da Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres, da shugabannin gwamnatoci fiye da 20 a ƙarshen wannan wata a wani taro kan siyasa da tsaro da ya ƙuduri aniyar ƙarfafa tasirin da China ke da shi a yankin, a cewar Beijing a ranar Juma'a.

Shugabannin ƙungiyar waɗanda ke wakiltar kusan kashi ɗaya bisa huɗu na duniya, za su gabatar da sabbin tsare-tsare na zurfafa dangantakarsu a lokacin da za su hallara a taron ƙolin ƙungiyar haɗin gwiwa ta Shanghai (SCO) a birnin Tianjin daga ranar 31 ga watan Agusta zuwa ranar 1 ga Satumba, kamar yadda mataimakin ministan harkokin wajen China Liu Bin ya shaida wa taron manema labarai kan shirye-shiryen taron.

Taron zai gudana ne tsakanin ranakun 31 ga watan Agusta zuwa 1 ga watan Satumba, 'yan kwanaki kaɗan kafin birnin Beijing ya gudanar da faretin soja mafi girma a cikin shekaru da dama, kuma la’akari da tsare-tsaren shugaban Amurka Donald Trump kan harkokin waje da cinikayya, musamman kan Isra'ila da Gaza, da batun haraji, taron ya janyo manyan masu ruwa da tsaki daga yankin kusa da China.

Manyan shugabanni daga ƙasashe mambobi ko kuma ƙasashen da za su halarci taron kamar Turkiyya da Belarus da Iran da Kazakhstan da Pakistan da kuma Vietnam na daga cikin waɗanda ake sa ran za su halarci taron.

Kazalika ana sa ran Firaiministan Malaysia Anwar Ibrahim zai halarci taron, bayan nan zai karɓi baƙuncin Trump da sauran shugabannin ƙungiyar ƙasashen kudu maso gabashin Asiya a Kuala Lumpur a watan Oktoba.

Mulkin mamaya da siyasar nuna iko

Shugaban China Xi Jinping zai gabatar da muhimman jawabai a wajen taron, wanda zai samu halartar shugabannin ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa.

A taron, China na fatan "ƙarfafa haɗin gwiwa...(da) tare da jajircewa da tsayin dakar ƙungiyar SCO, wajen mayar da martani kan al’amuran rashin tabbas a yanayin duniya," in ji Liu a yayin taron manema labaran.

"A duniyarmu ta yau, tsohon tunani na mulkin mamaya da siyasar nuna iko har yanzu suna da tasiri, inda wasu ƙasashe ke koƙarin fifita buƙatun kansu fiye da wasu, suna matukar yin barazana ga zaman lafiya da ƙwanciyar hankali a duniya," in ji shi yana mai ƙwatance da Amurka.

"Da jajircewa da kuma tsayin dakar ƙungiyar haɗin gwiwa ta Shanghai, za mu iya magance rashin tabbas da abubuwan da ba za a iya tantance zuwan su ba... wajen samar da yanayi mai kyau na zaman lafiya mai dorewa."

Za a kammala taron ne tare da rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi tare da fitar da sanarwar yarjejeniyar Tianjin, in ji shi.

A taron ƙungiyar SCO na shekarar 2024 da aka yi a Astana babban birnin ƙasar Kazakhstan, shugabannin sun amince kan kara haɗa gwiwa kan yaki da ta'addanci a yankin, da batun sabunta makamashi da kuma tattalin arzikin na zamani.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us